Baku shirya yin soyayya ba?

Ku koya yadda Idayat taki amincewa da wani dake son ta

Shekarun Idayat goma sha takwas da wani yazo neman ta da aure. A ranar daya faru, tana hanyar zuwa shagon da take siyar da abinci.

Mutumin ba bako bane a wajan ta. Dan kasuwa ne dake da shago a ungwar su. Daya tsayar da ita a ranar yayi mata magana, bata san abun da zai gaya mata kenan ba sanda yace:

“Idayat, makonni da yawa kenan da nake ta kallon ki. Na lura cewa kina da kaifi kuma ke budurwa ce mai kyau. Naga yadda kike aiki sosai. Ina sha’awar ki sosai. Ina son ki domin kina kwazon samun naki kudi ba kamar sauran yan mata dake rokon kudi daga mutane ba. Ina son na kara sanin ki. Idan kika bar ni zan so ki zama budurwa na kuma ki zama mata na a nan gaba.”

Idayat ta amsa shi tace:

Nagode da yabon da kake mun. Amma bana sha’awar ka.

Yayi kokari ya canza mata ra’ayi amma tace:

“Mallam, ban shirya yin aure ba. Shekaruna basu kai ba. Kuma bana son saurayi. Bana son nayi masaniyar dukkan wahala da damuwa dake zuwa da soyayya. Yanzu, ina son na kasance a kasuwanci na. Ina son na taimake mahaifiyata. Bana son komai ya jawo ni baya.”

Wannan bai hana shi damun ta ba. So daya ko biyu ya so ya tsayar da ita a hanya yayi mata magana.

Sai wata rana ya zo gidan su. Yayi wa mahaifiyarta magana. Yana son ya bayyana niyyar sa. Yayi alkawarin auren ta da kuma kula da ita. Mahaifiyarta ta yarda dashi.

Bayan haka, ta gaya wa Idayat ta yarda mishi. Tace yana da kudi kuma iyalin sa nada hankali. Ta gaya mata cewa tayi sa’an jan hankalin babban mutum kamar shi. Wannan bai canza ra’ayin Idayat ba.

Amma mahaifiyarta ta nace.

Sai ta yarda ta jure masa. Tana ta wayincewa kamar tana son sa na watani. A wani lokaci, ta fara canza halayyar ta masa. Mahaifiyarta ta lura canjin sai tayi mata gargadi.

Idayat ta roke mahaifiyarta kada ta bari ta aure shi. Ta gaya mata cewa bata son shi. Basu dace ba. Ta gaya mata cewa tana bakin ciki dashi. Har ta gaya mata yin aure da sauri zai hana ta yin abun da take so.

Da sa’a, ta iya canza ra’ayin mahaifiyarta. Mahaifiyarta ta bata izinin rabuwa dashi.

Tayi magana dashi. Ta gaya masa cewa bata sha’awa soyayyar kuma tayi ne saboda an takura mata.

Abun bai masa dadi ba. Ta bashi hakuri kafan ta karya soyayyar.

Yau Idayat ta maida hankali a kasuwancin ta. Ta koya muhimmanci a cikin yin magana.

Kuna cikin al’amari daya da Idayat? Iyalan ku ko abokan ku na takura muku ku fita da wani?

Yin magana zai iya taimakon ku. Ku gaya musu yadda kuke ji. Ku saka su fahimce abun da kuke so. Ra’ayin ku ne.

Wani babba na takura muku? Ku nema wani amintaccen babban mutum ya musu magana. Mai yiwuwa su saurare su.

Kun taba samun kanku a irin al’amarin Idayat? Ya kuka bi dasu? Ku gaya mana a sashin sharhi.

Share your feedback