Tsofofin maza na damu na

Ibukun da bamu labarin yadda ta rabu da tsofofi masu tashin ta

Shekaru na goma sha shida da makwafci na Lanre- mai shekaru ishirin da takwas ya fara bida na.

Ya fara da aika na sako. Duk sanda na taimake shi zai bani kyautar canjin. Na zata kawai yana da hankali ne.

Amma sai na fara lura cewa yana nuna wa ni kadai ne wannan halin. Baya haka da sauran yan mata a mahadin mu.


Wata rana ya kira ni gefe sai ya fara gaya mun wasu irin maganganu da ba gamsuwa. Yace na cika. Yace na fi sauran yan matan tsara na balaga.

Yace yana so na kuma yana so na zama budurwar sa.

Na gaya masa nayi masa kankanta.

Amma yace shekaru lamba ne kawai. Kuma shekaru na sun mishi.

Ya fara mun alkawari. Yayi alkawarin tura ni makaranta kuma da bani kudi koda yaushe.

Yace kada na gaya wa kowa akan maganan mu.

A lokacin na fara yin zargin sa. Naji labarin tsofofin yan maza kamar Lanre a kan Springster. Misali mai kyau shine labarin Dupe.

Na san cewa yakamata nayi hankali da shi.

Sai na roke sa ya kyale ni. Yaki ya saurarre ni. Kamar Dupe na yanke shawara na kai rahoton sa a wajan wani amintaccen babban mutum.

Na gaya wa mahaifiyata akan sa. Taji dadin dana gaya mata. Ta kusanta Lanre ta bashi kashedi ya guje ni.

Har tayi barazanan kai rahoton sa a wajan yan sanda idan ya kara mun magana.

Wannan al’amarin da Lanre ya koya mun akan muhimmancin yin magana.

Kuma na koya cewa kai rahoto wajan wani babba idan al’amari ya wuce gona da iri baya nufin cewa ni dakikiya ce.

Kuma zaku iya koya yin magana koda yaushe. Kada kuji tsoron cewa A’a. Kada kuji tsoron kai rahoton wani dake hana ku sakewa. Ku tuna cewa ba laifin ku bane.

Kun taba samun kan ku a al’amari irin na Ibukun? Gaya mana yadda kuka shawo kan sa a sashin sharhi.

Share your feedback