Babu komai a ciki!
Da nake shekaru goma sha daya, na samu jini a kampai na. Na rikice. Ban san daga ina ya zo ba ko kuwa abun dake faruwa da ni.
Wasu yan mata a kungiyar matasar mu sunce na fara al’ada ne. Na tambaye su ma’anar wannan, amma basu son sosai game da shi ba. Ina da tambayoyi sosai kuma bani da wanda zanyi wa magana.
Sai na karanta wani labari a kan Springster akan wata yarinya da ta gaya wa mahaifin ta akan al’ada. Na so labarin sosai domin ya bani karfin hali na tambaye mahaifina akan al’ada. Da farko, bai so yayi magana ba. Yana tunanin na kankanta. Amma dana gaya masa na fara al’ada, ya kwantar da hankalin sa ya cigaba da mun bayani.
Ya rarraba dukka bayanan da ni. Yan mata nada kwai da yawa, da bututu biyu dake daukan kwai, da kuma mahaifa daya. Idan yarinya ta fara balaga, kwai daya na barin daya daga cikin wajan da kwan suke yaje mahaifa. Rufin mahaifan na kara girma da jini da kuma nama, yana saka shi kauri da kuma tsaro. Wannan yana shirya mahaifan domin daukar haihuwa.
Idan kwan ya hadu da maniyyi, yana hada jariri. Idan kwan bai hadu da maniyyi ba, mahaifan na zubar da karin jini da nama. Sai ya fito ta farji. Ana kiran wannan al’ada ko kuwa jinin haila. Kawanyar al’ada na faruwa a kowane wata - Sai dai mace ta dauke ciki. Ko kuwa wa wasu dalilai kamar canjin nau’in abincin da kuma gajiya.
Bayan watani kadan, tattauna al’ada a makaranta. Samarin na sha’awar kara sanin akan sa, sai na gaya musu komai. Wasu yan mata na kunya, amma na gaya musu kada su ji kunyan yin magana akan al’ada. Kuma bai kamata kuyi ba. Al’ada alama ne cewa muna girma. * Idan aka zo akan al’ada, wa kuka fi so kuyi wa magana? Ku gaya mana a wajan sharhi.
Share your feedback