Ku tsaya da karfi, kada ku fid da rai

Ku cigaba da tafiya koda menene

Ni ce abun da za’a kira mai tsira daga abun da zai iya halakarwa.

Shekaru na biyu sanda mahaifina ya bar mu. A haka ni da mahaifiyata muka fara zama mu kadai.

Ina kaunar zama da mahaifiyata. Uwa ce na arziki. Duk da bata da kudi, tana tabbata cewa ban rasa komai ba.

Duk da cewa komai na tafiya daidai, akwai wani matsala daya. Mahaifiyata nada saurin fushi. Ta matsa mun rayuwa.

Na tuna wani rana da aka mun zargi cewa na kwana da yaron makwafcin mu. A ranar, tayi mun duka har na suma.

Kuma dana tashi, ta kara mun duka. A ranar na fara tunani ko ita ta haife ni.

Bayan wannan lamarin, mahaifiyata ta canza mun. kamar bata kauna na ne kuma. Bata so na a kusa da ita.

A wasu lokuta tana barazanan yanke alaka da ni. Kuma wata rana ya faru. Mahaifiyata ta yanke alaka da ni saboda naje gidan Inna na ba tare da izinin ta ba.

A haka na kasance mara gida. Bani da wani wajan zuwa sai gidan mahaifina.

Zama da mahaifina bai zo da sauki ba. Ba ya goyan payan samun ilmi. Yana son nayi aure kuma yana takura mun sosai.

Dana gaya masa cewa ban shirya yin aure ba ina son naje makaranta, shima ya yanke alaka dani.

Abubuwa sun zo mun da wuya har sanda naji akan wani kungiya dake taimakon yan mata. Sai na shiga kungiyar.

Suka horar da ni. Suka nuna mun yadda zan taimake rayuwa na. Domin su, na iya fara wani karamar sana’a, na koma makaranta, na iya ciyar da kai na kuma na iya siyan ma kai na sitira.

Rayuwa ya fara mun dadi.

Shekaru biyar sun wuce yanzu da abubuwan nan suka faru dani. Nayi girma kuma na zama mace mai karfi.

Shawara na wa yan mata dake masaniyar wannan irin abun shine su kara tsaya da karfi. Su yi hakuri. Kada ku daina amince da kanku koda ba wanda ke imani da ku.

In da dama, ku gwada yin wa iyayen ku magana. Ku gaya musu yadda kuke ji.

Ko kuwa zaku iya neman wata amintacciyar babba kuyi wa magana. Ku ga ko zasu iya taimakon ku yin wa iyayen ku magana.

Wani abu kuma da zaku iya yi shine neman kungiyoyi dake taimakon yan mata. Sai ku shiga.

Ku gaya mana akan iyayen ku. Me yasa suke da muhimmanci gare ku? Kuyi mana magana a wajan sharhi.

Share your feedback