Yar Springster mai karfin hali

Yadda na hana mai reno na tsangwama na

Ina makarantar firamare sanda na fara masaniyar tsangwama.

Ya fara bayan dana kai rahoton malamar mu zuwa shugaban makarantar mu. Wani dan ajin mu yayi kashi a wando kuma mai renon mu taki ta wanke masa. Tace ba aikin ta bane. Dukkan ajin ya dau wari amma taki tayi komai akan sa.

Shugaban makarantar mu ya shiga ajin mu sai ya tambaya dalilin daya sa ajin ke wari. Sai na gaya masa saboda dan ajin mu yayi kashi a wando ne.

Nan take ya tambaya dalilin daya sa mai aikin bata wanke mishi jiki ba. Tayi karya tace bata san cewa yayi kashi a wando ba. Sai na bude baki nace tana karya. Na gaya wa shugaban cewa ta sani amma taki ta wanke mishi jiki.

Shugaban makarantar mu ta kwabe ta. Tun daga ranar mai aikin ta tabbata cewa ta dame rayuwata.

Wata rana ta so ta mun karyar sata. Ta saka abincin wani a cikin jaka na. Dana bude jaka na sai naga abinci guda biyu. Sai nayi zato duk wanda ya ajiye shi zai zo ya dauka idan suna bukata.

Da nake cin abinci na sai wani yaro ya fara kuka yana cewa an sace mishi abinci. Sai da sauri mai renon mu tace ai taga abincin a cikin jaka na. Sauran mallaman ajin mu suka tambaye ni. Nace musu bani na sace ba.

Suka kai ni wajan shugaban makarantar mu. Ya tambaye ni yadda abinci a shiga jaka na. Na kasa basa bayani amma nayi karfin zuciya na kare kaina.

Na tsaya daram nace bani na sace abincin ba. Amma mai renon mu ta cigaba da cewa ni na sace abincin.

Shugaban makarantar mu ya yanke shawarar yin binciken al’amarin. Ya tambaye yan ajin mu, suka gaya masa cewa sun gan ni ina cin abinci na ne kawai. Har suka ce sun ga sanda na bar dayan abincin a jaka na.

Bayan binciken, shugaban makarantar mu ya gano cewa mai renon mu ne ta saka abincin a cikin jaka na. Abun daya saka ta fadin gaskiya shine don na tsaya da gaske. Ban saka hayaniyar ta ya tsorata ni ba.

Bayan al’amarin an dakatar da ita daga zuwa aiki. Na cigaba da zuwa makaranta ba tare da tsoro ba.

Duk da yake wasu ranaku zuwa makaranta nada wuya saboda wasu yara na tunatar dani da ranar. Wasu lokuta suna kira na barauniya, idan suka yi ina tabbatar cewa na kai rahoton su a wajan shugaban makarantar mu.

Abun dana koya daga wannan shine, yin magana idan abu mai muhimmanci ya faru. Wasu lokuta mutane baza su so kuyi magana ba. Amma wannan baya nufin cewa kuyi shiru. Idan kuka yi shiru mai yiwuwa ku shiga wani matsala.

An taba tsangwamar ku? Ku gaya mana abun da kuka yi akan sa a sashin sharhi.

Share your feedback