Stella ta tsara nan gaba cewa zata ci nasara a burin ta kuma kema zaki iya yi.
Da nake karama, ina son kallon mahaifiya ta idan tana shirin tafiya aiki.
Ina son zanunnukan ta da abayan ta. Na kosa nayi girma nima na samu aiki. Amma bana son na zama malamar koyarwa kamar mahaifiya ta. Ina son na zama madinki. Ina da burin yin wa mutane kyawawan kaya, kuma na kara sa mutane aminta da kansu.
Ina jin dadin bin mahaifiya ta wajan madinkin ta. Matan nada hankali, tana son dariya. Wata rana, na tambaye ta yadda ta koya dinki.
Ta gaya mun cewa sanda take shekaru na, tana yin wa yar tsanan ta kaya. Sai da tayi girma, taje makarantan dinki. Ta koya mun yadda zan yanke kyalen kaya. A nan take, na yanke shawara cewa zan fara da sauri nima.
A gida, ina yin zanen kaya a littafi. Ina kallon hotunan riguna a jarida, sai nayi irin su wa yar tsana na.
A shekaru goma sha biyar, na yaudara mahaifiya ta ta barni na fara koyan dinki. Nayi aiki da wata madinki dana hadu da a kasuwa da nake cafane da mahaifiya ta. Na koya da sauri domin ina ta gwaji da dadewa. Kafan a waigaya baya na fara yin wa mahaifiya ta kaya da sauran mutane. Na ajiyen kudi ma keken dinki.
Bayan makaranta, na shiga wani jami’ar koyan dinki. Na koya akan tsari, da irin irin jiki
Dana kai shekaru ishirin, na zama madinki. Na kara samun abokan kasuwanci. Na buga katin kasuwanci na.
Yanzu na samu nawa shagon. Aiki yayi mun yawa. Amma yana da daraja- mutane na cewa kaya na nasa su jin dadi. Ina farin ciki cewa na ci nasaran buri na.
Kin san inda kike son ki gan kanki nan da shekaru biyar? Koda menene muradinki, idan kika fara da sauri zaki fi jin dadi. Yafi ki fara abinda kike son kiyi a lokacin da kika san abun da kike so. Kada ki damu idan yafi shekaru biyar. Ki imani da kanki ko da menene. Ki gaya mana muradin ki a shafin sharhin mu.
Share your feedback