Mahaifiyar ki zata iya zama babba abokiyar ki

Zaki iya koyar abubuwa da yawa daga abokantakar ki da mahaifiyar ki

Wa zai iya zato cewa mahaifiya ta zata zama abokiya ta?

A da ina tsoron mahaifiya ta. Ina tunanin bata so na. Har sai da na fara al’ada.

Na rikice, ina tsoro. Ban san wanda zan wa magana ba amma nasan dole nayi wa wani magana da wuri.

Mahaifiya ta ce kawai ke nan kusa, sai naje na same ta duk da cewa ina tsoro, sai na gaya mata akan jinin dake fitowa.

Ta rungume ni sosai bayan dana gaya mata. Ta mun bayanin abubuwan dake faruwa da jiki na. Tace al’ada na ne kawai kuma ba komai. Ta gaya mun kada naji tsoro, sai ta taimake ni wanke jiki na.

Ta nuna cewa ta gane komai akan shi kuma ta bi shi da inganci.

Ta nuna mun yadda zan yi amfani da audugar al’ada. Har ma ta nuna mun yadda zan lissafa kawanyar jinin haila na.
Ta gaya mun kada naji tsoron zuwa nayi mata magana akan kowane abu.

Tace kada naji tsoron yin mata magana akan abun dake damu na. Tun lokacin nan, dangantaka na da mahaifiya ta ya karu. Ina mata magana akan abubuwa sosai. Tana bani shawara akan kowane abu, har da samarai ma.

Ta san abubuwa sosai. Ina rarraba wasu abubuwa da nake koya daga wajan ta da abokai na. Wasun su naji dama suna ke abokantaka da mahaifiyar su kamar yadda nake da mahaifiya ta.

Koda yaushe ina gaya musu su riga bude wa mahaifiyar su cikin su. A wani lokaci uwayen mu ma na yan mata. Sun masaniyan yawancin abubuwan da muke ji yanzu. Zasu fahimta.

Suna da abubuwa da yawa da zasu koya mana.

kina al’ajabin yadda zaki kara dangantakar ki da mahaifiyar ki? Gwada wadannan abubuwan;

  • Kiyi girki da ita. Kada ki jira sai ta roke taimakon ki a madafa.
  • Kiyi mata magana akan abubuwan da kike son yi da safgan ki.
  • Ki tambaye ta akan irin wakokin da take so, sai kisa ta ji irin da kike so.
  • Ki sa kuyi kallon wasan kwaikwayo da ake yi a talabijin tare.
  • Ki kwashe lokaci da ita
  • Ki koya yadda baza ki riga boye mata sirri ba.

Kina tsoron mahaifiyar ki ko wata babba a rayuwar ki? Kiyi mana magana akan abun da ke baki tsoro a shafin sharhin mu.

Share your feedback