Ina da babban buri ga rayuwata ta gaba

‘Yan mata na iya zama shugabanni su ma!

Duka faɗin duniya ‘yan mata na yin abubuwan bajinta kuma su na ƙarfafawa wasu yin haka. Ga guda biyu nan… Yarinyar da ta ɗauki matsayi a kan FGM Lillian Mwita, daga Kenya, mai baki ce, mai ƙwarin gwiwa kuma marar tsoro wajen tsayawa a kan abin da ta yi imani a kansa. “Ba zan yarda a yanke mun ba, koda suna kallona a matsayin bare ba ko a’a.” A shekaru tara kawai, lokacin da aka fuskanceta da kaciyar mata ta gudu daga gida ta nemi mafaka tare da masu yaƙi da kaciyar mata FGM. “Ni ƙarama ce. Ina da babban buri domin rayuwata ta gaba kuma abin da ya dameni yanzu shi ne ilimi,” ta ce. Yarinyar da ta ƙi yarda da tashin hankali Joyce Mkandawire ta ga ‘yan mata waɗanda ake ƙarfafa masu gwiwa su yi jima’i da maza (waɗan da ake kira kuraye) a ƙasarsu, Malawi. Kura ba su saka kariya, wannan ya sa na san ‘yan mata da suka kamu da HIV sabo da kuraye,” ta yi bayani. Ƙiyawarta ta karɓi mummunar al’ada, Joyce ta yanke shawara ta yi wani abu a kan wannan kuma ta kafa Cibiyar Ƙarfafa Gwiwar ‘Yan mata. Juriyarta da sha’awar son taimakawa a kawo canji na haƙiƙa ga ‘yan matan Malawi, canji zuwa abin da ya fi kyau wanda wata Joyce ɗin ta jagoranta – Shugabar Ƙasa Joyce Banda. ‘Yan mata ba za su sami nasara ba idan su na zaune a cikin tsoro. Daga ƙirƙirar fage na tsira zuwa dokoki masu ƙarfi, kawo ƙarshen tashin hankali ga ‘yan mata shi ne mataki na farko na kawo ƙarshen talauci a duniya. Jagoranci na bukatar ƙarfin hali. Ga wasu shawarwari na yadda za’a fara.

Share your feedback