Ruyuwata ba ta da alƙibla

Na samo hanya ta

Rayuwa cikin talauci da kuma takaitattun damammaki, ‘yan mata da yawa na fafutuka domin nemo mafita. Wannan labarin ɗaya daga cikin ‘yan matan ne. Suna na Mabreidy, shekaruna 16 kuma ina zaune a Jamhuriyar Dominika, a wani tsibiri na Kogin Caribbean. Garinmu, Cabarete, ya zama tamkar wata aljanna ce a duniya. Mutane na zuwa daga duk faɗin duniya domin ganin kogunanmu da kuma sananniyar igiyar ruwa a duniya wadda ake wasan sulu a kanta. Aikace-aikacen yawan-buɗe-ido na da kyau, amma babu isassu. A yanayi na rashin kudi, duk sai mu ji bamu da gata.

Mahaifina mashayi ne – tamkar sauran mutane a can. Yana yawan dukan mahaifiyata. Ni da ‘yan uwana muna jin tsoron samun rauni lokacin da ransa ya ɓaci.

A makaranta na yi ƙoƙarin yin ƙawaye sabo da ina matuƙar jin kunya da kuma tsoro in riski mutane masu shekaruna. Har ta kai ina faɗa da sauran ‘yan mata kuma in yi rigima a gida. Na maƙale. Bana samun ko wane tallafi domin jarraba wani abu sabo domin kowa ya damu da tasirin ɓaci a tare da ni. A ko da yaushe ina ji ana cewa, “Yi mana shiru, Mabreidy, “A’a, Mabreidy, “Yi shiru, Mabreidy.”

Mahaifiyata ta ji ina ƙorafi cewa ba ni da abin da zan yi, sabo da haka ta yi min rijista zuwa masaukin lokacin bazara domin ‘yan mata. Na fargaba. To amma a ranar farko mun kasance cikin annushuwa kuma muna koyon sababin abubuwa, misalin wasan kwaikwayo da rawar Fina-finan Indiya. Na fara yin sababbin ƙawaye masu yawa kuma daga baya na yi murmushi! Gidauniyar Mariposa DR ta koya mana yadda za muyi magana da turanci da kuma yadda za muyi iyo a ruwa da kuma yadda zamu tsayawa kanmu. Kuma sun ƙarfafa mu da muka kammala karatunmu, mu yi wasanni kuma mu yi rayuwa mai kazar-kazar.

Shirin bai ƙare da masaukin bazara ba. Mun ci gaba da haɗuwa muna koyon sababbin abubuwa. Mun koyi yadda ba zamu lalata kanmu da ƙwayoyi ko giya ba. Na koyi cewa rayuwa ta fi karfin fafutuka kawai.

Yanzu na san cewa ina da zaɓi masu yawa fiye da tafiya da maza waɗanda za su iya dukana ko cutar da ni.

Dangantakata da mahaifana ta sami ci gaba sabo da na zamo cikin farin ciki kuma na samu ƙwarin gwiwa. Babana (mahaifina) har yana zuwa ya kalli tserena na kan ruwa. Yana kirana “mace mai yaƙi a kan ruwa”! Har na zamo yarinya ta farko ‘yar Dominica a garinmu da ta koyi wasan jirgi na kan ruwa! Yanzu ina cikin farin ciki idan ina kan kogi. Ban san zan sami wannan mafarki ba. Yanzu na gane cewa zan iya shawo kaina da kuma zuciyata – a ciki da kuma wajen ruwa.

Ina alfahari cewa ina da baiwa kuma zan iya taimakawa wasu ‘yan matan su nemo tasu. Lokacin da nake koyawa sauran ‘yan mata yadda za suyi iyo a ruwa na gaya masu su manta da abin da mutane za su faɗa, ko da su na yi miki ba’a. Muna da ƙarfin da zamu ƙirƙiri rayuwarmu ta nan gaba, mu yi abubuwan da iyayenmu mata ba su sami damar yi ba. Daɗa karatu dangane da labarin Mabreidy a grassrootsgirls.tumblr.com

Share your feedback