Abubuwa guda biyar daya kamata kowane yarinya nada a lokacin al’adar ta

Tafiyad da lokacin ki na wata

Suna na Amina, shekaru na goma sha uku.

A asabar daya wuce, na fara al’ada na. Ina ta jin tsoro. Duk jini yayi mun datti da kampai da riga na. A guje naje na same mahaifiya ta saboda nayi tunani zan mutu ne.

Ta gaya mun ba komai kada naji tsoro. Tace yana nufi cewa yanzu jiki na ya shirya balaga kuma na haifa yaro idan na kara girma na shirya tada yara.

Ban gane ba. Bani ma da saurayi. Ya zan fara shirin haihuwa!

Mahaifiya ta tace ba haka bane. Baya nufin cewa zan dauke ciki. Kawai dai jiki na ya balaga. Yanzu kowane wata, mahaifa na na shirin daukan yaro. Zanen mahaifa na na kara kauri. Idan ban dauke ciki ba, zanen na rage kauri. Shine wannan jinin da nake gani.

Mahaifiya ta tace yawancin yan mata na ganin al’adar su bayan kowane kwanaki ishirin da takwas. Ta bani wani karamin kalanda domin na riga duba kwanakin. Sai ta kara bani wani karamin jaka, ta kira sa jakar al’ada. Tace na rike sa kulun, saboda idan al’ada na yazo a lokacin da ban tsammani ba.

Ga abubuwan dake ciki:

  1. Audugan al’ada: Tace wannan nada muhimmanci sosai. Yana hana jinin datti da kaya. Kuma yana saka ni walwala da kuma bushewa.
  2. Takardar bayan gida: Ina amfani da wannan a al’amarin da audugan al’ada na ya kare ne. Zan yi amfani da takardar al’adar domin na hana kai na jikewa kuma ya hana jinin datti da kaya na har sai na samu karin audugan al’adar.
  3. Karin kampai: Idan al’adar ki yazo ba zato ba tsammani, jini zai iya yin datti da kampan ki. Yana da kyau ki samu wani mai tsafta, saboda idan ya faru sai ki canza.
  4. Maganin ciwon ciki: A ranar farkon al’ada na, ina ta jin wani zafi. Mahaifiya ta ta kai ni wajan kantin shan magani. Mai kantin ta bani maganin ciwon ciki. Ta gaya wa mahaifiya ta yadda zan sha su. Mahaifiya ta ta bani kashedi nayi hankali idan ina shan maganin.
  5. Audugan kampai: Suna nan kamar audugan al’ada, amma karami da kuma siriri. Mahaifiya ta tace, zan iya amfani dasu a karshen ranakun al’ada na, idan ya rage nau’i.

Gaya mana akan ranar farko da kika gan al’adar ki a shafin sharhin.

Share your feedback