Ga gaskiyar
A matsayin matasa, al’ada ne kuyi sha’awar jima’i. Shiyasa wannan tambayar - Na rabu da budurci na? - zai iya zuwa tunanin ku sau daya ko biyu. Kada ku damu. Zamu taimake ku.
Wa yawancin mutane, budurwa mace ce da bata taba yin jima’i ba. Amma ba haka bane. Yin jima’i na nufin abubuwa daban-daban wa mutane dabam, saboda haka kuma budurci zai iya ma’anar abubuwa dayawa. A sakamakon haka, babu wani yarjejeniyar ma’anar budurci.
Mutane da yawa na tunanin cewa budurwa mace ce da fatar farjin da ba’a taba ba. Wannan fatar farjin wata fata ne dake rufe bakin farjin macen da bata taba yin jima’i ba. Ana haifan wasu yan mata da fatan farji mai kauri, wasu kuma ana haifan su da fatar fariji mara kauri. Mutane na fadin cewa idan azzakarin namiji ya mike fatar farjin a lokacin jima’i, toh wannan yana nufin cewa mace ta rabu da budurcin ta.
Duk da haka, fatar farjin zai iya mikewa ta wasu hanyoyi kamar hawa keke ko kuwa ta motsa jiki. A ce fatar farjin ku ya mike sanda kuke motsa jiki. Wannan yana nufin cewa kun rasa budurcin kenan? A’a! A yanke dogon zance dai, mai yiwuwa samun fatar farji bashi bane hanya mafi kyau da za’a bayyana ma’anar budurci.
Gaskiyar shine, babu wanda zai iya fadin ko mace ko namiji na nan da budurcin su ko basu da. Har likitoci ma ba za su iya fadi ba. Baza ku iya fadin ko mutum na nan da budurcin sa ba ta yadda kamanin sa yake ba, ko yadda suke magana ko kuwa halayyar su. Duk da haka wasu mutane na kunyatar samari domin suna nan da budurcin su. Idan wani ya kunyata ku domin baku rabu da budurcin ku ba ko, ko kuwa kunyi, ba daidai bane. Kada ku bari wani ya saka ku jin bakin ciki domin abun da kuka yi ko kuwa abun da baku yi ba.
A karshe, ba kome ko kuna da budurcin ku ko baku da. Abun muhimmancin shine baku yi abun da zai hana ku walwala ba. Ko kuwa wani abu da baku son yi. Abun muhimmancin shine girmama jikin ku kuma ku tabbata kuna tare da wanda ke girmama ku da jikin ku.
Kuna da yancin yanke shawara game da jikin ku. Idan kun fara yin jima’i kuma kuna son ku daina, toh ba komai. Idan kuma baku son ku fara yin jima’i, ba komai. Jikin ku ne, ra’ayin ku ne. Bayan dukka wannan, zai fi ku jira sai zaku iya bi da sakamakon, misali, daukan ciki da cututtukar jima’i. Ku duba nan domin ku kara koya: http://ng.heyspringster.com/sections/my-body/i-think-im-pregnant
Banda wannan, akwai abubuwa mafi muhimmanci a rayuwa. Kamar cimma burin ku. Saboda haka, jeki ku rubuta wannan takardar. Ku koya yadda ake rubuta tsarin dokokin kwamfuta. Ku nema maganin ciwon daji. Ku mamaye duniya.
*
Kuna da wasu tambayoyi akan budurci? Ku sake ku tambaye mu a sashin sharhi.
Share your feedback