Kyawu na zuwa a launi daban daban

Kyawu ba akan yadda kamanin mu yake bane kawai, yana nufin abun da ke cikin zuciyar mu

Mai yiwuwa kina jin mutane na fadin abubuwa kamar, “wancan yarinyar tayi baki da yawa. In da ita fara ce da tayi kyau.”

Ko wasu tallace tallace da ake yi a talabijin, na nuna kamar fararen mata sun fi mafificin.

Amma kyawu ba akan launin fatar ki bane, ko dogon gashin ki. Kyawu ba akan dan kankanin jiki bane. Kyawu ba akan yadda kamanin mu yake bane kawai.

Akan abun dake cikin zuciyar mu ne. Akan yadda halayyar mu yake ne. Akan yadda muke daukan mutane tamkar ne. Idan muka dauke mutane da kyau, a take muna da kyau a wajan su.

Wasu mata na maida launin fatar su ya zamato fari saboda suna son mutane suyi tunanin suna da kyau.

Maida launin fata ya zamato fari bai da kyau. Wasu ma’adanin kimiyya dake maida launin fata fari na iya sanadin Matsalolin lafiyar jiki. Wasu ababanda da aka kera na maida launin fata ya zamato fari zai iya jawo tabo, da ciwon daji na fata. Wasu ma zasu iya kisa.

Wasu mai na jiki na maida launin fata fari na amfani da kalmomi kamar “saiwowi na itace ko dabi’ance, domin su sa mu Imani cewa suna da kyau.

Gaskiyar shine, ana samun abubuwa da yawa a dabi’ance, amma baya nufin cewa duka suna da kayu a jikin mu.

Muna da kyau yadda muke. Idan muna da farin ciki da aminta, kyawun mu zai yi kyalli wa kowa ya gani.

Kina ganin kyawu akan kamani ne kawai? A’a. Asalin kyawu na cikin yanayin dabi’un mutum a rayuwa da kuma halayyar mutum. Kada ki raina kamanin ki ko na wasu.

Mutane na dariyan launin fatar ki? Kiyi mana magana akan sa a shafin sharhin mu.

Share your feedback