Abubuwan da zaki iya yi da kuma abubuwan da baza ki iya yi ba dan ki hanna kurajen fuska a lokacin al’adan ki

Kurajen fuska a lokacin al’ada ne wannan kankani abubuwa dake fitowa a fuskan ki kaman tabbo, gishirin fuskan da sauran su

Tunanin ku (3)

Daga rashin samun sinadarin kimiyya mai kyau zuwa canji jikin ki wanda yasa sa gaban jikin ki me mai ya fitar da mai sosai fiye da yadda jiki yake bukata, duk su ke kawo kurajen fuska a lokacin al’ada.

Abu daya da ya kamata ki gane shine wannan al’amarin na faruwa da kowa, kada ki damu ko kiji kunya idan ya faru da ke. Abun dadin shine, zaki iya kula dashi da wadannan abubuwan daya kamata kiyi da kuma abubuwan da bai kamata kiyi ba.

Kada ki taba su

  • Dannawa ko taba kurajen zai sa datti a cikin fata ki, kuma zai sa shi kumbura, da kuma sa miki ciwo wanda zai bar miki bakin tabbo a kyakkyawan fuskan ki. Mun san cewa tafiya da tabbo a fuska ba abun da zaki so bane shi yasa zakiyi kokari ki gyara fuskan ki. kiyi kokari ki cire hanun ki daga fuska. Tabawa da dannawa zai sa shi bacewa sosai.

Ki tsaftace fuskan ki

  • Wanke fuskan ki da ruwan zafi da sabulu mara karfi da safe da kuma dare, zai taimake ki da yawan kurajen. Kada ki manta ki shafa mai idan kika gama wankewa

Yi amfani da tiririn ruwan zafi

  • Zaki iya amfani da tiririn ruwan zafi a fuskan ki. Ki saka ruwan zafi a kwano, sai ki kai fuskan ki kusa dashi, saboda hayaki (tiririn) dake fitowa daga ruwan zafin zai shiga fuskan ki. Ki rufe kanki da tawul saboda hayakin ya shiga fuskan da kyau, kuma kiyi kokari kada ki kai fuskan ki kusa da ruwan zafin sosai saboda kada ki kona ki.

Ki sha ruwa sosai

  • Ruwa na korin datti daga jiki. Yana sa fata kyau da Karin Karin lafiya. Shan ruwa da safe idan kika tashi bacci na da kyau a jiki.

A mako na gaba zamu nuna kiki abubuwan da zaki iya amfani a gida ki gyara fuskanki. Ki shiga yanki sharhin mu na maganganu ki gaya mana yadda kika bi da kurajen fuskanki.

Share your feedback

Tunanin ku

munata jiran cigaban bayanin haryanxu shiru

March 20, 2022, 8:04 p.m.

menene abunda xan iya amfanidashi domin kore taban kuraje afuskana?

March 20, 2022, 7:58 p.m.

Bani Da Kurajin Fuska Amma Tayaya Zanguje Musu

March 20, 2022, 7:57 p.m.