Abinci da zai kara karfafa halayyar ki

Cin abinci zuwa hanyar rayuwa mai lafiya

Wasu lokuta idan ina bakin ciki, ko ina haushi, ko ina gajiye. Zan je wani shago na siyo nau’in abinci mai zaki, ko cake ko kuwa daskararren madara mai zaki. Amma bayan na gama ci, bana jin dadi. A gaskiya, wasu lokuta, ina kara jin bakin ciki.

Yar uwar mahaifiya ta likita ce. Na tambaye ta idan akwai wani irin abinci dake da dadi da kuma zai kara mun lafiya.

Ga abinci guda biyar da tace na gwada

Ayaba
Ayaba na kara miki karfi duk lokacin da kike jin gajiya. Suna kara taimakon jikin ki sarrafa wani kimiyya da ake kira serotonin. Wani kimiyya ce na dabi’ance dake taimakon kara gyara halayyar ki.

Kwakwa
Mai da ake samuwa a kwakwa nada sinadarin dake gina jiki. Abun ingancin shine kwakwa na taimakon jikin ki sarrafa kuzari! Saboda ki samu karfin aiki dukka ranar.

Kwai
Kwai nada sinadarin dake gina jiki da kuma nau’in ma’adanin kimiyya. Kuma suna da sinadarin da ake kira VItamin B. Kwai na bada kuzari dake da dadewa. Zasu saki aiki da kyau a gaba dayar rana.

Kifi
Kifi nada sindarin dake gina jiki kuma bai da mai sosai. Kuma yana kyau a wajan kara wa kwakwalwa lafiya. Kuma yana kara dabi’ance kimiyyar jiki dake taimaka saka ki jin mafi jijjiga.

Wake
Wake nada sinadarin gina jiki dake bada kuzari kuma zai kara miki karfi. Kuma suna da sinadarin gina jiki dake taimakon jikin ki tafiyad da gajiya.

Yana da muhimmanci mu duba abun da muke ci. E mun san cewa ba abinci bane tushen farin ciki amma zai iya taimako.

Idan kika ci abinci da kyau, zaki samu lafiya.

Idan kina da lafiya zaki samu cikakken kuzari kuma wannan zai saka ki a cikin halayya mai kyau.

Share your feedback