Labarai al’ada masu bada dariya

Wa yace baza ki iya dariya a lokacin da kika kunyatar da kanki?

Yin al’ada ba komai bane, amma wasu lokaci ba zai sanar da zuwan sa ba. Wannan zai iya kunyatar dake! Duk mun taba samun irin lokacin nan da zamu ji kaman kasa ya bude ya hadiye mu. Ga wasu labarai masu bada dariya na yan mata kaman ke da al’adan su yazo bada sanarwa ba.

Masaniya al’ada na daya kunyatar dani shine ranar dana fara al’ada na. A wajan biki ne a gidan yar uwan mahaifiya ta. A cikin wasa da cin abinci na lura cewa bana jin dadi sai naje bandaki. Na fahimta cewa al’ada na yazo. Nayi tafiya da hankali na same yar uwa ta sai ta gaya mun naje na same maman mu. Dana same ta na kashe murya na ina mata magana sai wata yar uwan mahaifiyata ta lura yadda nake shiru sai ta kwala wa mahaifiyar ta kira daga dayan dakin “shin lafiya da yarinyan nan? Sai mahaifiyata tayi ihu gaba dayan iyalai na naji, “tana lafiya, ta dai fara al’ada ne!” sai kunya ya kama ni! - HAUWA

Naje kasuwa na siya takalmi. Ina fita daga shagon takalmin sai wani dan saurayi ya fara kwala mun kira. Na zata yana son ya matsa mun lamba ne sai na share shi. Sai yayi ihu “ina kiran ki kina share ni, ji yadda kike, kayan ki yayi datti da jini”. Kawai Sai nayi addu’a kasa ya bude ya hadiye ni. Mutane duk suka sa mun ido. - MARYAM

Daya daga cikin labarai masu bada dariya na al’ada na shine lokacin da nayi amfani da fale fallen takarda sai ya fadi. Ya dauke ni lokaci kadan kafan na lura cewa ya fadi. Ina naiman shi kafan naga makwafci na son ya dauka daga kasa ya harbe yaron sa dashi dan bai san ko menene ba saboda dare yayi. Sai nayi sauri na dauka da hankali na kai bandaki na zubar da shi.AMINA

Idan kina son ki kauce irin wadannan halin, ki karanta Makala mu akan yin kalanda na al’ada. Shawara ne mai kyau kina rike da audugan al’ada a ko wanda lokaci saboda idan al’adan ki yazo bada sanarwa ba.

Kina da wani labarin al’ada mai bada dariya? Ki gaya mana a shafin sharhin mu.

Share your feedback