Yadda zaki bi da warin baki

Hanyoyi guda shida zuwa nunfashi mai kamshi

Kiyi tunanin mutane na rufe hancin su idan kina magana. Ba tunani mai dadi bane ko?

Nunfashi mai wari zai iya kunyatar dake.

A Yawancin lokuta, kwayoyin cuta ne ke sanadin warin baki ko kuwa abun da muke ci. Musamman idan bamu buroshi da kyau ko a kowane lokaci.

Busashen baki na iya sanadin sa.

Amma ma wasu mutane, ciwo ne da ake kira Halitosis dake bukatan hanyar jinyar da cutar.

Kina da nunfashi mai wari? Kin san wani mai nunfashi mai wari? Ga wasu abubuwa da zai yi taimako.

Ruwa da hadin lemun tsami
Lemun tsami zai iya taimaka hana girman kwayoyin cutar. Idan kina son ki rabu da warin baki, ki matse lemun tsami daya a cikin moda daya na ruwa. Ki saka gishiri kadan. Ki wanke bakin ki kowane rana da hadin kafan kiyi bacci.

Man goge baki
Zaki iya tambaye wani babba ko kantin magani su baki shawarar man goge baki mai kyau. Ki gwada buroshi da man goge baki so daya a rana.

Cin gam
Ki hana busashen baki ta cin gam ko kayan zaki marasa sikari.

Ki ci ‘ya ‘yan itatuwa masu sa koshin lafiya da kuma ganye
Hanyar daya mafi inganci da zaki cire kwayoyin cuta daga bakin ki shine idan kika ci aful guda a rana. Shima yana hana busashen baki.

Kisha ruwa
Ki ajiye bakin ki jike da ruwa ta hanyar shan ruwa sosai.

Ki naima taimako
Idan warin nunfashin ki ya cigaba bayan ki gwada dukka wadannan abubuwan, kiyi magana da wani babba da kika yarda da. Zaki iya ziyarta wani asibiti a al’ummar ku kiyi korafi.

Kina da siddabaru akan yadda zaki kasha warin nunfashi? Gaya mana a shafin sharhin mu.

Share your feedback