Yadda zan bi da sinadaran kimiyyar jikin na.

Samun ma’anan dukka canjin

Balaga zai iya yi wa yar mace tauri. Yawancin mu na jin bakin ciki ko rikita ko haushi ba da dalili ba. Jikin mu na canzawa a hanyoyi da bamu gane ba. Bamu iya gane ma’anan komai kuma.

Ga labarai masu dadi: ba kome bane. Kina girma kuma jikin ki na canzawa. Shikenan. Muna da siddabaru da zasu taimake ki bi da abubuwa da kyau. Muje zuwa:

  • Idan nonuwan na bunkasa, ba komai bane idan daya yafi daya girma. Mai yiwuwa su kama juna nan gaba, kuma mai yiwuwa baza suyi ba. Ba komai bane. Yawancin mu bamu da nonuwa iri guda. Kada ki damu idan nonuwan abokan ki sunfi naki girma ko naki yafi nasu girma. Mun zo da siffa daban-daban da yanayi. Kina da kyau a yadda kike. Ki so kanki koda menene.
  • Ranaku kafan al’adan ki, mai yiwuwa ranki na yawan bacewa. Mai yiwuwa kina marmarin wasu irin abinci ko kuwa nonuwan ki na laushi. Ana kiran wannan PMS (tgamayyan matsalolin al’ada). Canjin a matakin sinadaran kimiyyar ki ne ke sanadin su. Rage cin sikari da mai na taimako. Ki guje kayan zaki. Kiyi aikacen motsa jiki mara wuya domin ki fitar da damuwa. A bugu da kari, ki sha ruwa sosai kuma ki samu isasshen bacci. Bada jimawa ba zaki fara farin ciki da dariya.
  • A shekarun ki, ba komai idan kina burin sanin akan jima’I. kuma wasu lokuta idan kika yi tunanin wani yaro da kike so, kina jin wani iri tsakanin kafafun ki. Shaukin na lilo daga hanun hagu zuwa dama. Kada kiji tsoro ko kiji kunya. Ba abun dake damun ki. Kiyi magana da wani babba da kika yarda da. Zaki kara jin daidai.

Shikenan. Yanzu ki huta. Kasancewa budurwa nada dadi.

Ya kuma kike bi da sinadarin kimiyya na jiki? Gaya mana a shafin sharhin mu.

Share your feedback