Yadda zaki tsaftace kanki

Rayuwar marasa halitta dake sanadiyyar rashin lafiya

Mataki na farko na rayuwa mai lafiya shine tsaftar jiki dana muhalli.

Samun tsaftar jiki dana muhalli marasa kyau zai iya saki ciwo domin zaki jawo wa kanki halitta dake sanadiyyar rashin lafiya.

Kuma lafiyar jiki shine kyauta mai inganci da zamu iya bawa kan mu.

Kiwon lafiya yana fiye da wanke hakora ko wanka a kowane rana.

Ga wasu hanyoyi da zaki tsaftace kanki kuma ki samu lafiya.

  • Kada ki saka kampan ki fiye da so daya. Ki wanke su a kai a kai.
  • Ki riga wanke bayan kunnuwan ki idan kina wanka.
  • Ki zub da audugan al’adar ki yadda ya kamata. Ki saka shi a bakar leda, ko kuwa fale fallen takarda kafan ki zubar dashi.
  • Ki lura da gashin dake karkashin hamatan ki da farjin ki. Zaki iya aske shi ko kuwa ki rage shi idan ya cika. Muna yawan zufa sosai a wadannan wajajen. Wannan zufan zai iya jawo miki warin jiki. yana da muhimmanci ki wanke gashin wajan nan. Zamu iya samu ya yan zufa idan bamu lura da gashin hamatan mu da farjin mu ba. Yanke shawarar aske ko rage gashin ko kuwa kin aske gashin idan ya cika na wajan ki.
  • Ki lura da farcen ki. Ki rage su domin suyi tsafta. Ki cire dattin dake karkashin farcen ki.
  • Kiyi kokari kada kiyi amfani da kayan ki kamar kampai, da rigar mama, da rezar yanke gashin ki da sauran mutane.
  • Ki wanke farjin ki kowane rana da ruwa. Kada kiyi amfani da sabulu ki wanke farjin ki.
  • Ki saka kaya masu tsafta. Ki wanke kayan ki koda yaushe. Ki tabata sun bushe kamar yadda ya kamata kafan ki saka su.
  • Bayan kin gama amfani da shadda ki goge daga gaba zuwa baya saboda ki guje cuta.
  • Koda yaushe ki wanke hanun ki kafan kiyi amfani da shadda da bayan kin gama amfani dashi, kafan kici abinci, kafan ki fara dafa abincin, bayan kin taba datti da kuma bayan kinyi tari ko atishawa.

Kina da wani damuwa akan tsaftar jikin ki dana muhallin ki? Akwai wasu karin abubuwa akan tsaftar jikin ki da muhallin ki da kike son ki sani? Kiyi mana magana a shafin sharhin mu.

Share your feedback