Smart girls can love fashion too
Kuyi tunanin wani abu da kuke so. Yin karatu, ko kayan yayi, ko darasin lissafi, ko wasan kwallo, ko kuwa dukkan su. Koda menene, ba lailai sai kun bada bayanin dalilin da yasa kuke son sa ba. Maimaiko, ku maida hankali a kan zama mafi kyau a shi. Eh Zaku iya!
Amma idan baku kara aiki ba, baza ku kware a burin ku ba. Zaku iya farawa da tambayan tambayoyi. Ko kuwa yin magana da wadanda suka kware da shi. Zaku iya rijista a wani aji ko kuwa ku karanta akan sa a yanar gizo gizo. Kuyi gwaji sosai har sai kun kware.
Wasu mutane zasu gwada kashe muku jiki. Zasu ce bai kamata ‘yar mace ta zama mai koyan ilmin kimiyya ba. Ko kuwa yarinya mai hikima baza ta iya son kayan yayi ba. Suna tinanin idan yarinya na son irin abubuwan nan, toh yana nufin cewa bata da hikima. Wannan ba gaskiya bane. Zaku iya son abubuwa da yawa. Kuma zaku iya kware a dukkan abubuwan nan. Duniya babban waje ne wa kowa ya bi burin sa.
Babu abu mai kyau dake zuwa da sauki. Saboda haka kuyi hakuri. Kada ku dame kanku. Ku cigaba da tafiya da hankali a lokacin ku har sai kun cimma burin ku. Baku takara da kowa
Zai yi wa mutane sauki suyi imani daku idan kuka yi imani da kanku. Ku rike kanku a sama. Ku malaka ra’ayin ku. Kuyi alfahari da kanku. Wata rana mutane zasu kalle ku suce “Eh dama mun san cewa zata iya mamaye duniya!”
Saboda haka mu tashi mu ci nasara a dukkan abun da muke so, yan mata! Koda yin zane zane ne, ko waka, ko harkar kudade, ko kuwa ilmin kimiyya. Mun hadu a kowane rana.
Menene babban burin ku? Gaya mana a wajan sharhi.
Share your feedback