Ina ganin ina da ciki

Menene abun yi

Sannu Babban Yaya,

Akwai babban matsala! Wasu lokuta da suka wuce, na kwana da saurayi na Chude. Ba muyi amfani da kwararon roba ba, amma ba komai bane. Muna kaunar juna kuma mun amince da juna sosai.

Sai a wata daya gabata, na fara jin gajiya sosai kowane safe. Na zata saboda aikin gida da nake yi ne. Shiyasa ban damu ba. Sai kwankwaso na ya kara kauri kuma nonuwa na suka yi taushi. Har Inna na tana mun tsiya akan sabon canjin jiki na.

Amma yanzu al’ada na yaki zuwa! A farko, ban damu ba fa. Wasu lokuta yana dan jinkiri na kwana daya ko biyu. Sai kwanaki uku suka wuce, kuma naji shiru! A lokacin na san cewa akwai matsala.

Babban Yaya, ina ganin ina da ciki! Ban san abun yi ba ko kuwa wanda zan yi wa magana. Nayi tunanin gaya wa Chude, amma ina ganin wannan shawarar bai yi ba. Akwai wani cibiyar lafiya a al’ummar mu. Ina son naje wajan na duba, amma bana son labari na ya kai kunnuwar Inna na.

Wannan ba abun da na tsara wa rayuwa na ba kenan. Shekaru na goma sha shida ne kawai! Dan Allah ki taimake ni. Babban Yaya! Zan haukace.

Nagode,
Susu


Sannu Susu,
Bara na fara da cewa ba ke kadai bace. Yan mata da yawa a gaba dayan duniya suna samen kansu a irin wannan al’amarin. A karshe, sun fito da karfi, da wayo, da kuma inganci. Kuma kema zaki yi.

Cikin da ba’a shirya ba na iya zuwa da wuya. Amma idan kin san abun yi, abubuwa zasu iya zuwa da sauki.

Na farko, Yakamata ki tabbata cewa kina da cikin. Saboda haka, kije kiyi gwaji. Zai taimaka idan kina da wata amintaccen babba dake kusa dake. Zata kai ki asibiti kuma ta baki goyon baya a gaba dayan lokacin.

Innar ki na kama da wace zata gane al’amarin ki. Mai yiwuwa ki gwada amince da ita. Zaki yi mamakin yadda zata amsa ki. Mai yiwuwa ma ta taba samun kanta a irin wannan al’amarin. Saboda haka zata san yadda zata jagora ki. Koda za tayi bakin ciki mai yiwuwa ta goya miki baya.

Idan kina ganin kamar baza ki iya yin wa Innar ki magana ba, akwai wata amintaccen babba da zaki iya aminta da? Idan babu kowa, zaku iya zuwa wani kungiya da ake kira Education as a Vaccine. Suna tafiyad da wani gidan waya dake taimako akan jima’i, ciki da kuma sauran matsalolin lafiyar jiki. Suna nan a bude daga litinin zuwa Juma’a daga karfe tara na safe zuwa karfe biyar na yamma. Ki kira su a wanna layin 08027192781 domin samun wannan goyon bayan da kike bukata. Ki kula cewa za’a cire miki kudin waya kuma suna da tabbaci, baki bukatan gaya musu sunnan ki.

Amma bayan dukka wannan, akwai mutum daya da ya kamata kiyi wa magana: shine Chude. Yana daukan mutane biyu domin samun yaro. Ciki ba nau’in mace bane kawai. Idan eh da gaske kina da ciki, yakamata Chude ya dauke nau’in yaron sa. Yafi ki gaya masa abun dake faruwa.

Kafan kiyi masa magana, kiyi gwajin abun da kike son ki gaya masa. Zai taimake karfafa ki. Ki zabi wani lokaci da wajen da zaki iya walwala kiyi masa magana.

Na gaba, Da ke da Chude na bukatan neman wani asibiti mai kyau da zaku je tare (tare da wata/wani amintaccen babba in da dama) domin kuyi wa wani likita magana. Zasu yi miki gwajin. Idan kina da ciki, zasu gaya miki yadda zaki lura da kanki. Kada ki damu, kinji? Komai zai kare da kyau.

Ki tuna idan baki san wani asibiti kusa dake ba, zaki iya yin wa mutanen nan na Education as a Vaccine.

Ki tuna, yin jima’i ba tare da kwararon roba na iya jawo ciki da sauran cutar jima’i. Hanya na kwarai da zaku guje wadannan shine idan baki yi jima’i ba. Idan kina da wasu tambayoyi kuma, dan Allah kiyi wa wata kwararren likita magana.

Mun gode da kika raba labarin ki damu, Susu. Muna fatan samun karin lafiyar ki. Muna miki fatan alheri.

Da kauna,
Babban Yaya

Kun taba masaniyar wani abu kamar haka? Gaya mana a wajan sharhi.

Share your feedback