Baki yi laitin balaga ba; Ke balagaggiya ce
Akwai lokuta da rayuwa ke kasancewa kamar wasannin al’ada da ake gudanarwa bayan shekaru hudu. Dukka abokan ku sun ga al’adar su ko. Kuma baza su bari ku sha ruwa ba! Sun cigaba da magana akan sa. Lokacin daya fara, yadda ya fara, da kuma tsawon lokacin sa.
Kuna ji dama kuma zaku iya yin nishadi kamar su. Amma kuna shekaru goma sha shida kuma baku fara ganin al’adar ku ba ko. Don haka, kawai zaku yi murmushi ku girgiza kai kuyi shiru. Kuna al’ajabi ko naku lokacin zai zo.
Kun san mene? Zai zo! Rayuwa ba gasa bane. Abubuwa basu faruwa wa daukkan mu a lokaci daya. Mu yan mata na ganin al’adar mu na farko a shekaru dabam dabam: Takwas, goma sha daya, goma sha uku, goma sha shida, har goma sha takwas! Jikunan mu daban ne.
Babu shekaru daya dace da wanda bai dace ba a ganin farkon al’ada. Babu lambar yabo da ake bawa yan mata da suka fara al’ada da sauri a ko ina. Saboda haka kada kuyi bakin ciki. Kuyi tabbaci ku karfafa kanku.
Koda yaushe ku tuna: Ba abun dake damun ku. Kada ku canza nau’in abincin da kuke ci ko kuwa kuyi wasannin motsa jiki. Kada kuyi abubuwa da bai dace domin ku sa al’adar ku yazo. Al’adar ku zai zo idan lokaci ya kai. Amma idan kuna bukatan kwararren tabbaci, ku ziyarta wani likita da zaran kun samu lokaci.
Kuma idan kuka ga farkon al’adar ku, zaku yi mamakin sa. Zaku fara amfani da audugan al’ada kamar abokan ku. Zaku gano dalilin daya sa suke damun ku akan sa. Amma a karshe, zaku ga cewa ba komai bane. Domin ku koya abun yi a lokacin farkon al’adar ku, ku karanta labarin Amina a nan
Amma a yayin da, kuyi wa abokan ku farin ciki. Ku saurare labarin su na al’ada kuma kuyi dariya dasu. Kafan ku sani lokacin rarraba labarin ku zai zo. Kuma abokan ku zasu goya muku baya.
Kun ga farkon al’adar ku ko? Gaya mana a wajan sharhi.
Share your feedback