Ku tsaftata farjin ku

Komai na nan da lafiya a can kasa

Farjin ku ba waje bane mai muhimmanci kawai. Yana da saurin ankarewa da wani alama ko canjin ma. Wannan yana nufin cewa kuna bukatan kula da shi na musamman domin rigakafin kamuwa da cuta.

Kuna al’ajabin yadda zaku fara? Kun zo wajan kwarai. Ku bi wadannan dabarun, zasu taimake ku:

1. Kada ku
Wanke farjin ku da sabulu da kuma sauran sabulun ruwa da ake amfani a wanke farji ko kuwa sabulai masu karfi. Zasu iya tada halittar ma’aunin jikin ku. Ku samu karin bayanai akan sabulun ruwa a nan


Kuyi
Ku wanke farjin ku da ruwa mai dumi, da kuma sabulu mara karfi da kamshi. Baku bukatan wanke shi da dukkan karfin ku. Farjin ku na wanke kansa daga ciki ta wannan farin ruwan dake fitowa daga farji.

2. Kada ku
Bushar da farjin ku da wani tawul mai taushi ko wani mai datti da aka yi amfani da bayan wanka. Zai iya jawo wa fatan ku ciwo.

Kuyi
Ku goge farjin ku da tawul mai laushi da tsafta.

3. Kada ku
Saka matsatstsen kampai ko wando mai yaddin leda ko roba. Zaku iya saka ku zufa da doyi.


Kuyi
Saka kampai mai tsafta da aka yi da yaddin auduga. Suna shanye zufa sosai kuma zasu saka fatan ku ya sha iska.

4. Kada
Kada ku goge farjin ku daga baya zuwa goba bayan kunyi bayan gida. Zai tura kwayan cuta dake duburar ku zuwa farjin ku.


Kuyi
Ku goge farjin ku daga gaba zuwa baya koda yaushe. Idan kuna da fata mai saurin ankarewa da wani alama ko canjin, kuyi amfani da fallen takarda domin kuyi rigakafin kamuwa da cuta. Idan kuma zaku amfani da ruwa ne, ku bushar da farjin ku kafan ku saka kampai ko wandon ku. Kuma, kada ku manta ku wanke hannayen ku da sabulun duk sanda kuka yi amfani da bayan gida.


5. Kada ku
Kuyi fargaba idan farjin ku na fitar da wani ruwa mai launin madara. Ba sabon abu bane. Al’adan jiki ne.

Kuyi
Kuje kuga wani likita idan farjin ku na fitar da ruwa mai launin ruwan kwai ko kuwa launin kore, idan yana wari ko kuwa yana kaikayi.

6. Kada ku
Aske gashin farjin ku da dakusashshe reza ko kuwa sanda aske gashi mara tsafta. Ko kuwa ku aske gashin saboda kowa nayi. Babu kamani daya na farji. Idan kuna son ku aske gashin, ba komai. Idan kuna son ku bar gashin, ba komai. Jikin ku ne, ra’ayin ku ne. Tunda dai wajan nada tsafta, baku da matsala.


Kuyi
Aske gashin farjin ku da sanda aski mai kaifi da kuma tsafta. Na farko, ku rage gashin da wani karamin almakashi mai tsafta. Sai ku aske sauran gashin da hankali saboda kada ku yanke kanku. Idan kuka gama, ku shafa Aloe Vera a wajan domin ya sassauta shi. Sai kuyi ajiyar sandar aske gashin a wani waje mai tsafta domin ku guje kwayan cuta.


Toh gashi nan, yan mata! Yanzu ku nuna wa farjin ku kauna.


Kuna da wasu dabaru na kula da farji? Ku rarraba da mu!

Share your feedback