Babban jagora wa yan mata dake kan girma kamar mu
Balaga. Abun burgewa ne wa wasun mu. Amma wa sauran, zai iya zama abun rikitarwa. A kowane rana wani sabon tambaya na zuwa. Daga “ meyasa nake bakin ciki?” zuwa “meke faruwa a can kasa?” idan kin taba jin irin haka, baki bukatan damuwa. Ba abun dake damun ki.
Ga wasu abubuwa da zaki sa rai kiga da jikin ki ke canzawa.
Canje canjen halayya
A lokacin balaga, kwan ki na fara sarrafa wani sinadarin kimiyya na jiki da ake kira estrogen. Wannan yana saka halayyar ki su ringa zuwa sama da kasa. Minti daya kina farin ciki, minti na gaba kuma kina bakin ciki ko fushi. Duk shaukin ki na ko ta ina. Samun isasshen hutu, da bacci da kuma wasan motsa jiki zai taimake ki jin dadi. Cin ‘ya ‘yan itatutwa, da ganye, da kuma kwayoyin hatsi zai kara miki lafiyar jiki. Shan isasshen ruwa ma na taimako.
Kara girma a tsawo da nauyi
Bayan al’adar ki ya fara, zaki kara tsawo kamar inci biyu ko uku a shekaru kan gaba. Ana kiran wannan girma. Duwaiwan ki zai kara fadi, kwankwason ki zai kara matsewa. Hanayen ki, da cinyar ki, da kuma bayan ki zasu kara kauri. Kada ki damu. Halitta ne a gurin mu idan muna da dan mai a jiki. Ki kula da daidaita cin abinci, zaki samu lafiya.
Yin zufa
Gashin farji, dana hamata, da kuma kafafun ki. Wani abu dake faruwa idan sinadaran kimiyyar jikin ki suka karu. Saboda haka, idan kina wanka ki tabata kin wanke wajajen nan da hankali. Kiyi amfani da tularen feshi na jiki dake hana zufa da warin jiki. Ki saka kaya masu tsafta kuma wanda akayi daga auduga. Zasu taimake jikin ki yin nunfashi da kyau.
Sha’awan jiki
Kin san wannan yaron nan makwafcin ki mai bada haushi? Bai bada haushi kuma, ko? Mai yiwuwa kina sha’awan shi. Mai yiwuwa kin fara tunanin jima’i. Akwai wannan kawazuci da kike ji a can kasa. Baki bukatan jin kunya. Ba komai bane. Duk al’ada na girma ne. kiyi magana da wani babba da kika yarda da. Zai taimake.
Wace sauran hanyoyi ne kuke canzawa? Gaya mana a shafin sharhin mu.
Share your feedback