Ku nuna wa jikin ku kauna yan mata!

Hanyoyi guda biyar da zaku lura da jikin ku

Kamar matasa muna son muyi gwaji musamman idan yazo game da kamanin mu.

Gaskiyar shine wani sabon kamani na iya karfafa tabbacin mu kuma, ya saka mu jin dadi da kanmu. Amma yana da muhimmanci muyi kokari kada mu sak ya dauke hankalin mu.

Ga dalilan daya sa muna bukatan yin kula idan muna yin gwajin wani sabon kamani.

A wannan shekarar fatan mu nada dan laushi. Ya kamata mu kula da abubuwan da muke amfani da.

Saboda muna goyon bayan ku, ga wasu dabarun kyawu:

Lebe
Lebe shine daya daga cikin yankin jiki dake saurin ankarewa da wata alama ko canji a jiki. Suna bushewa da wuri. Muna baku shawara kada ku lasa ko ku fere idan ya bushe. Zai iya bata muku lebe.

Kada ku saka jan baki a busashen lebe.

Idan leben ku ya bushe ku shafa masa sikari da man zaitun. Kuma zaku iya gwada man kade. Wannan zai taimaka ya cire busasshen fatar. Zaku iya yin amfani da vaseline bayan nan.

Gashi
Ku wanke gashin ku akalla so daya a mako. Kuyi amfani da sabulun wanke gashi kuma ku tabbata kuyi tururin gashin ku koda yashe- zaku iya yin naku a gida da mai kamar man zaitun, ko na kwakwa ko kuwa man kade. Kuma zaku iya wanke gashin ku da sabulun solo. Idan fatan kan ku ya bushe, kuyi masa tururi. Kuyi amfani da man kade.

Fuska
Yin amfani da kayan adon fuska sosai zai iya toshe ramukan fuskan ku, kuma ya jawo muku kurajen fuska. Saboda haka idan kuna son canza kamanin ku ku gwada amfani da kayan ado dabam-dabam. Idan kuka yi amfani da hoda mai maiko da kuma jan baki yau, toh gobe ku canza kuyi amfani da hoda mai boye tabo da kuma hoda mai gari. Kafan kuje bacci, ku wanke adon fuskan ku da kyau da sabulu koda yaushe.

Farce
Kada kuci farcen ku. Zaku iya samun cuta. kwayoyin cuta dake karkashin farcen ku zasu iya shigan bakin ku kuma su jawo muku ciwon ciki.

Cin farcen ku zai iya bata siffar su.

Ku tabbata kuyi amfani da abun yanke farce idan zaku gyara farcen ku.

Fata
Muna da fata dake da saurin ankarewa da wani alama fiye da manyan mutane. Yakamata mu lura da yadda muke bi da fatan mu. Fatan ku nada maiko sosai? Ku riga wanka sosai.

Fatan ku na bushewa sosai? Ku shafa masa mai koda yaushe.

Abu mafi kyau da zaku iya yin wa jikin ku shine shan ruwa sosai. Wannan zai hana shi bushewa kuma zai saka shi haske.

Dabara mafi kyau akan kyawu da zamu iya baku shine yin murmushi. Murmushi zai saka ku yin walkiya kuma ya kara muku aunin darajar ku.

Kuna da wasu dabarun kyawu?Ku rarrraba da mu a sashin sharhi.

Share your feedback