Muna canzawa, suma suna canzawa!

Maza ma na masaniyar balaga kamar mu

Dukkan mu mun taba masaniyar wannan. Zamu karo da wannan yaron da muka dade bamu gani ba sai muyi mamaki! Ya aka yi yayi tsawo haka? Ya aka yi muryan sa ya kara zurfi? Ya aka yi ya kara kyau ba zato ba tsammani?

Na farko, ku kwantar da hankalin ku yan mata! Ba komai bane. Maza ma na masaniyar balaga. Amma jikin su na dan canzawa daban da namu.

Ga abubuwan da kuke bukatan sani:

Gashi
Kamar yan mata, yan maza nada gashi a hammatar su, da azzakarin su, da kuma hannuwa/kafafun su. Amma kuma suna samun gashi a fuskan su da kirji. Kamar mu, sinadarai a cikin jikin su da ake kira sinadaran jinsi, dake sanadin wadannan canjin. Kuma suna saka su zufa sosai. Wasu lokuta wannan na saka su wari.

Murya
Idan maza na girma, tsirkiyar muryar su na kara girma. Wannan ne ke saka muryar su ya canza. Na farko, muryan su na kara karfi da zurfi. Wannan zai iya saka su yin kara mai ban dariya. Bayan kwana kadan, muryan su zai kwanta sai ya kara zurfi.

Fuska
Bamu kadai bane ke fama da kurajen fuska. Balaga ma na samun samari a fuska. Zufan su da wani gaba na jiki dake fid da mai zasu iya toshewa kuma su sanadin kurajen fuska masu zafi. Wannan zai iya kunyatar dasu, kamar yadda yake mana.

Jiki
Wannan ne yanki mai nishadi. Idan balaga ya same samari, jikin su na fara bunkasa. Wasun su na kara tsawo a cikin shekaru biyu ko uku. Ana kiran wannan feshin girma. Wasu samari na farawa da rashin natsuwa. Suna zub da kiban su. Kirjin su da kafadar su na kara fadi. Gabobin su na bunkasa. Hannayen su da kafafuwar su na kara girma. Duk wannan na kara saka mu sha’awar su. Kuma wannan ba komai bane.

Sassan Jima’i
A lokacin balaga, maza ma na fara masaniyar kawazucin jima’i. Suna samun tashin azzakari, shine lokacin da azzakarin su yake cika da jini har ya saka shi tashuwa. Wasu lokuta idan maza suka samu tashin azzakari, suna sake maniyyi. Ana kiran wannan kawowa. A lokacin jima’i, maza na kawowa sai su sake maniyyi, dake yin iyo zuwa cikin mahaifan mu. Idan ya hade da wani kwai a wajan, zamu iya daukan ciki.

Kuna da burin sanin akan jima’i da daukan ciki? Kuyi wa wani amintaccen mutum magana ko kuwa wani dake aiki a asibiti.

Ku tuna, dukkan mu na masaniyar balaga. Saboda haka, yan maza na masaniyar balaga kamar mu. Idan jikin ku bai fara canzawa ba, kada ku damu. Balaga na farawa a lokuta daban wa kowa.

Kun lura wasu canji a maza da kuka sani? Gaya mana a wajan sharhi.

Share your feedback