Lafiyar jikin ku shine arzikin ku

Dabaru da zasu kara inganta ku

Idan akwai abu daya da bai kamata kuyi wasa da ba shine, lafiyar jikin ku. Idan kuna da lafiya, zai yi muku sauki ku cimma burin ku. Zaku ji dadi da kanku– da kuma komai. Ga wasu dabaru da zai taimake ku gujen rashin lafiya:

Tsafta da kuma sabunta
Bara mu fara da masu saukin. Ku wanke hannayen ku koda yaushe. Kuyi wanka so biyu a rana, da safe da kuma dare. Ku kula da gaban ku da kuma hammatar ku. Kada ku taba fuskan ku,da idannun ku da kuma bakin ku. Ku goge bakin ku so biyu a rana. Kuyi tari ko atishawa a cikin wani kyale ko a kan hannun ku, kada kuyi sa a tafin hannun ku. Ku wanke hannun ku bayan kun yi amfani da bandaki ko kuwa kwandon shara. Dukkan wadannan zasu hana kwayoyin cuta zuwa kusa daku.

Kuci abinci masu kyau
Baza ku taba yin kuskure ba idan kuka samu tsarin abinci mai kyau. Kuci ‘ya yan itatuwa da kuma ganye sosai. Suna tare da sinadaran lafiya da zasu taimaka hana lalacewar kwayoyin jikin ku.
Gwanda, lemu, da kuma karas misalai ne masu kyau. Kuma zaku iya cin nama, kifi, wake da kuma kwai. Suna tare da sinadaran gina jiki da zasu taimaka su warkar da ciwo da wuri. Na karshe, a maimakon cin kayan zaki, zaku iya gwada cin kuli-kuli ko dankali. Abinci zai iya kasance da lafiya da kuma santi.

Abun halitta mafi kyau
Kuna ji kamar kuna da mura, ko kuna tari ko ciwon makogwaro? Toh,mai yiwuwa wannan ya taimaka. Ku saka gishiri a cikin ruwan zafi, sai ku kuskura shi a makogwaron ku. Sai ku saka kwano da ruwan zafi a karkashin hancin ku na minti kadan ko kuwa kuyi wanka da ruwan zafi. Tiririn ruwan zafin zai bude muku kofan hancin ku. Ku tuna ku tabbata cewa ruwan bai da zafi sosai. Ku guje kayan sanyi. A maimako, ku nika citta, ku hada shi da zuma, sai kuyi hada kofin shayi ku sha. Sai ku huta ku zauna a dumi. Idan baku samu lafiya ba, kuje ku ga likita nan take.

Ku tsirata kanku
Yin jima’i zai iya baza ku wa cuta kamar kanjamo da kuma kabba da ciwon sanyi. Kwaroron robo zai iya taimaka wajan hana wannan. Duk da haka, hanya guda za zaku guje cutar jima’i shine ta rashin yin jima’i. Akwai tambaya? Kuyi wa wani amintaccen babban mutum kamar innar ku ko wata babba. Ko kuwa kuje wajan wani likita tun da wuri.

Toh shikenan, Sprinsters. Menene dabaru mafi kyau wa lafiyar jiki? Gaya mana a nan kasa.

Share your feedback