Yadda zaku bi da kunyatar jiki

“ A lokacin da suka je kasa, mu muje sama” – Michelle Obama

Yadda zaku bi da kunyatar jiki

Kalmomi nada karfin iko. Suna tsaya da mu fiye da muke tunani. Saboda haka idan wani ya gaya mana wani magana mai zalunci akan jikin mu, yana nitsewa har cikin kashin mu. Muna jin wani iri kuma muna al’ajabin abun da muka yi mara kyau.

Ana kiran wannan kunyatar jiki.

Yana faruwa da yan mata kamar mu a kowane rana. A lokuta kamar haka, yana taimako ku tuna cewa ba laifin mun bane.

Baza mu iya iko da abubuwan da mutane ke fadi mana ba. Abun da zamu iya iko da shine martanin mu. Ga wasu dabaru da zai taimaka karfafa mu.

Kuyi magana kuma ku kare kanku
A lokaci na gaba idan aka kunyatar jikin ku, ku bawa mai laifin mamaki da murmushi. Ku gaya musu, da hankali, cewa kuna kaunar kanku a yadda kuke. Kuyi musu bayanin dalilin daya sa kalmomin su ke da lahani. Ku tunatar dasu su zama masu hankali. Kada ku bi halayyar su. Kada ku zage su, koda menene.

Kada ku fashe
Kuyi kokari kada kuyi ihu ko kuka. Wannan ne hakika abun da suke so kuyi. Kada ku bari su san cewa sun raunata ku. Maimakon haka, ku gwada kirga daga daya zuwa goma a cikin zuciyar ku. Zai taimaka kwantar da hankali ku. Bayan nan, idan kuna son kuyi magana, kuyi a murya dai dai.

Kuyi tafiyar ku
Wasu lokuta shiru ne amsa mafi kyau. Ga misali, mai yiwuwa ku fuskance wani kungiyar kunyatar da jiki. A wannan al’amarin mai yiwuwa mayar da martani bashi bane abu mafi kyau. Baya nufi kuna da rauni. Yana nufin kun fi su girma da hankali.

Ku kai rahoto
Kada kuji tsoron yin magana. Ba wanda ke da ikon raina ku. Ku koya yadda zaku kai rahoto kowane mutum mai zalunci ko kunyatar jikin ku ko na wani da kuka sani a wajan wani amintaccen babban mutum.

Idan wani ya kunyatar jikin ku, suna magana akan su ne. Baku ba. Kuna da kyau da kuma musamman. Ku kasance kanku na asali kuma kuyi farin ciki.

Kuma, ku gaya wani abu mai kyau yau. Zaku yi mamakin yadda zasu ji dadi.

An taba kunyatar jikin ku? Ya kuka amsa? Gaya mana a nan kasa.

  • tsira
  • tabbaci
  • kyawu