Kin Fara Al' Ada?

Ga Wasu Bayanai:

Tunanin ku (8) Kin Fara Al' Ada?

Ko wane wata bututun mahaifa na sakin ƙwai, kuma shimfiɗar mahaifarki (mahaifa) tana daɗa kauri domin shiryawa ko kwan zai sami haɗuwa da maniyyi (wato lokacin da ki ka sami ciki). Idan ƙwan bai sami haɗuwa da maniyyi ba a wannan watan, wannan shimfiɗar mai kauri sai ta fashe kuma ta fito cikin wasu kwanaki kaɗan – wannan ita ce lokacin al’adarki. Da zaran kin fara al’ada jikinki zai iya ɗaukar ciki kuma ki sami yaro idan ki ka yi jima’i. Dole ki tabbatar kin kare kanki daga ɗaukar ciki idan ba ki shirya samun jariri ba. Abin da aka saba ne ki sami ciwon ciki kaɗan lokacin al’ada. Zai taimaka idan ki ka saka jakar ruwan ɗumi a cikinki. Yana da kyau ki motsa jiki kaɗan kamar tafiya maimakon ki zauna a wuri guda. Idan ciwon yayi yawa, ki tuntuɓi likita. Idan ba’a samun audugar mata kuma ki na amfani da tsumma, ki tabbata cewa tsumman yana da laushi, wankakke kuma wanda ya bushe sosai. Idan ba ki yi al’ada ba, jikinki yana aika miki da saƙo ne, sabo da haka ki lura. Yi ƙoƙarin in abinci mai lafiya kuma ki samu isasshen bacci. Idan ba ki yi al’ada ba a wasu watanni kaɗan, ya kamata ki je ki ga nas ko likita

An kashe Yin sharhi a wannan makala a wannan lokacin.

Tunanin ku

maryam

Kamar Da Yaushe Ne

2 years, 4 months kwanaki da suka wuce
rahoto Mayar da martani

0 Mayar da martani

Rabiyatu

I Dan Mace Tana Da Ciki Kuma Sei Ta Sadu Mijinta Har Yakaye Ga Mijin Ya Kawo Maniyi In Maniyin Zai...

2 years, 8 months kwanaki da suka wuce
rahoto Mayar da martani

0 Mayar da martani

kara karanta sharhi