Ya zan rijista a shafin yanar gizo gizon?
Idan zakiyi rijista a shafin GEM Nigeria, ki latsa akan tambarin rijista na na’urar mu, cika bayananki wanda ya dace da kuma kammala rijistan ki. Za’a rijistar karin bayanin ki a cikin na’uran mu. Ki tabbata cewa lambar sirri na na’uran ki da sunan ki da kika zaba a na’ura nan masu sauki ne kuma zaki iya tuna dasu, ko kuwa ki rubuta su a litafi saboda kadda ki manta dasu idan zaki shiga shafin yanar gizo gizon mu.
Zan iya yin sharhi ba tare da sunana na nunawa ba?
Zaki iya boye sunan ki idan zakiyi sharhin.
Ya zan shiga takaran labari kuma menene za’a bawa wanda ya samu nasara a gasan?
Idan zaki shiga takaran kalmomi, ki tura labarin ki. kada ki manta ki bada sunanki da kuma bayanin ki a karshen labarin ki saboda mu tuntuba ki idan kika samu nasara. Wanda suka samu nasara zasu samu katin waya na dari biyar, a kowane fasahar da suke so.
Zan iya zabin amsa da yawa?
E, zaki iya zabi amsa mai tarin yawa ama ya daganta da zaben. Wasu zabe na bukatan amsa daya kawai. Duk da haka, Yakamata kiyi rijista kuma ki shiga shafinki dan ki shiga zaben. Kadda ki manta ki amfani da suna da lambar sirri na na’ura mai sauki saboda ki tuna idan zaki shiga shafin ki.
Idan na shiga zaben, za’a wallafa amsa na da suna na a shafin yanar gizo gizon na springster?
Idan kika shiga zaben, baza a wallafa sunan ki da lambar wayan ki a shafin yanar gizo gizon.
Idan naga wani labari da nake so, ya zanyi sharhin?
Zaki iya sharhin a labarin da kike so idan kika koma kasan shafin, latsa tambarin sharhi, bada sharhin ki sai ki mika shi. Kada ki manta sai kinyi rijista da kuma shiga shafin ki kafan kiyi sharhi a shafin yanar gizo gizon mu.
Zan iya tura labari da za’a wallafa a shafin yanar gizo gizon ku?
E, zaki iya! Tura mana labarai ki ta takaran kalmomi. Kowane wata, muna da sabon darasin da ake magana saboda mu tabbata kin dawo shafin yanar gizo gizon mu dan samun ra’ayi akan abubuwan da zaki iya rubuta mana.
Zan iya gyara kuskure idan na tura labari?
Baza ki iya gyaran kuskuren Sharhin da aka riga aka tura ba.
Ya za’ayi na goge sharhin bayan na tura?
Baza ki iya goge Sharhin da aka riga aka wallafa ba.