Springster yana tattara bayani (”bayanai”) game da kai don taimaka maka cim ma yawanci da Springster da kuma sauran kayayyakin mu. A lokacin da muna tattara bayananka, muna tabbatar da cewa za a riƙe su da tsaro kuma muna girmama sirrinka a kowane lokaci (a lokacin da kake yin amfani da wurin gizo da kuma idan ka tsaya).
Mun ɗauki alkawarin samar maka da wannan tsaro da kuma sirri a kowane lokaci, haka kuma muna buƙata a yi wannan a ƙarƙashin ire-iren dokoki da yawa (kamar waɗanda suke game da Kariya da Sirri na Bayanai) da suke sanya ga Girl Effect (’uwar’ Springster), a zaman babban ofishinmu da yake a Birtaniya.
Bayanai da muke tattarawa daga gare ka.
Idan ka yi rajistan yin amfani da Sprinster, sabanin duk wurin da kake a duniya, za mu tattara da kuma raba wasu bayanai game da kai. Wannan bayani yana haɗa wani suna mai amfani (na ra’ayinka), shekararka, jinsinka, kalmar sirri taka, da kuma tambayoyin tsaro naka. Idan ka hallara cikin bayar da sharhi, ƙuri’o’i da nazarori, ko gasa, za mu ajiye wancan bayanin kuma. Idan kana yin amfani da injin taɗi namu, haka kuma za mu ajiye sunan Facebook naka a cikin bayanan da muke tattarawa.
Bayanin da muke tattarawa domin kana yin amfani da Springster.
Wataƙila mu tattara bayani game da wacce ƙasa kake a lokacin da kake yin amani da Springster da kuma kayayyaki masu alaƙa, kamar injin taɗi namu. Bugu da ƙari, ta ƙarin hanyoyin fasaha, kamar Kukis, haka kuma ƙila mu tattara ƙarin bayani game da wurinka (alal misali ƙauyenka ko garinka). (Shi kuki wani ƙaramin rubutaccen fayil ne da ake saukar da shi a kan kwamfutarka ko wayar hannu taka a lokacin da kake iso ga wani wurin gizo. Yana bawa wurin gizo ɗin damar gane na’urarka da kuma ajiye wasu bayanai game da fifikanninka ko ayyuka da suka gabata).
Muna yin amfani da Kukis don bin sawun abubuwa kamar yawan mutane daga wurinka na gamagari da suka yi amfani da wurin gizon. Ba za mu taɓa yin amfani da bayanin wurinka don neme ko ko samu gidanka da gaske ba sai da ka nemi wannan takamaimai kuma ka ba mu dalla-dallan izininka.
A lokacin da ake hallara cikin ƙuri’o’i da nazarori ko yin amfani da injin taɗi na Springster, wataƙila mu nema ka raba bayani game da kanka da kuma rayuwarka ko ka gaya mana game da ra’ayoyinka da kuma ƙwarewarka. Kana iya zaɓan wane bayani za ka so ka bayar. Za mu yi amfani da wannan don taimaka mana tabbatar muna bayar da sabis mafi kyau na Springster da kuma ire-iren bayani mafi amfani.
Bayanai da ƙila ka samar mana da su ba sai mun tambaya daga gareka ba.
Wani lolaci, kana iya shiga wata tattaunawa a kan Springster ko daga cikin sauran namu kayayyakin. A lokacin da kake ba da sharhohi a kan wurin gizon, kana da zaɓin saka sharhohinka ban da suna. A lokacin da kake sharhin, kana iya ba da bayani game da kanka, sha’awowinka, iyalinka, abubuwa da suka faru da kai, abubuwa da za ka so yi, tunaninka da kuma yadda kake ji. Koda yaushe za mu yi ƙoƙarin sa ido a kan waɗannan sharhohi don tabbatar da cewa ana iya cire komai da bai dace ba ko da ake iya yin amfani da shi don gane ka. Amma don Allah kada ka manta da cewa nauyinkane kada ka raba da bayanai wanda zaisa a iya gane ka a lokacin bayar da sharhi a kan Springster. Muna yin amfani da bayanai da aka samar da su a cikin sharhohi don gane da ƙarin kyau waɗanne batutuwa da kuma labarai da suke ba wa mutane masu yin amfani da Springster sha’awa, yanda Springster yake yin amfani da bayani da aka raba ta namu kayayyaki a cikin rayuwa ta kullum nasu, da kuma don bunƙasa sabis-sabis kamar namu injin taɗi.
Idan kana yin amfani da injin taɗi ta hanyar Facebook Messenger, bayani da kake rabawa a kan injin taɗi za a danganta shi da furofayil na Facebook ɗinka. Ba za a raba wannan bayani tare da jama’a ba kuma za mu yi amfani da shi kawai don taimakawa da kuma koyar injin taɗi domin bunƙasa yanda yake samar maka da bayani.
Waɗanda muke raba bayaninka tare da su.
Farkon gungun mutane da suke iya ganin kowanne a cikin bayanan da muka tattara daga gare ka su na ma’aikatan Girl Effect (da kuma waɗanda suke yin aiki a madadin Girl Effect), dukka waɗanda suke sa hannu a kan yarjejeniyoyi da kuma tabbartawar za su riƙe bayaninka asirrance kuma waɗanda ake buƙata su bi ƙa’idoji masu tsanani sosai wajen sirri da tsaro. An zaɓi ma’aikatanmu bias cancanta, an ba su horo da kuma sun shirya domin ku a zaman membobi na al’ummar Springster.
Bugu da ƙari, wasu lokutan mukan yi aiki da wasu kamfanoni ko hukumomi don taimaka mana haɓaka da kuma gudanar da Springster. Waɗannan “wasu dabam” ɗin suna iya samun damar gano bayananka, amma aikinsu ba don a yi bitarsa ba kuma ana bari kawai su ga bayananka domin su iya taimaka mana wajen haduwa da mutane a cikin ƙasasshen da muke yin aiki ta hanya mafi kyau da kuma sauki. Wannan gungu na “wasu dabam” ɗin za su kuma sa hannu a kan wata yarjejeniya tare da mu game da asiri da kuma tsaro da suke sanyawa bisa abin da muke iyawa da kuma wanda bazamuiya ba da bayananka. Kuma, muna yin hankali sosai wajen zaɓin namu wasu dabam ɗin.
Wasu dabam ɗindamuke raba bayanai sun haɗa:
Kana iya buƙatar wani cikakken jeri na wasu dabam ɗin tare da wa muke raba bayanai idan kana sonsanin wasu ababe tuntuɓe mu a dataprotection@girleffect.org.
Idan kana samun daman zuwa Springster ko namu injin taɗi ta hanyar Facebook ko idan kana duban wurin hanyar zamantakewa na Springster kamar Facebook, Instagram, BBM ko Line, ya kamata kuma ka yi bita nasu manufofin sirri don ganewa kanka yanda suke yin amfani da bayananka.
Abin da kake iya yi.
Kana iya roƙa mu share gaba ɗaya dukkan bayanai da muke da su game da kai, wannan yana nufin ba za ka iya ci gaba da yin amfani da dukkan sabis-sabis ɗin ba kuma. Ana kuma kiran wannanHaƙƙin Mantauwa naka. Idan ba muda wani dalili kwakkwara na riƙe wani daga cikin bayananka ba, muna farin cikin share dukkansu. Amma, akwai wasu lokutan da muna yin amfani da bayanannka don maƙasudin ƙididdiga ko nazari ko don taimakawa Girl Effect cim ma burinsa wajen ƙarfafa wa ‘yammata gwiwa. A cikin waɗannan halaye, ba za mu share dukkan bayananka ba, za mu cire kawai dukkan abubuwan da sukan iya bada bayanan ka (wana ake kira kuma ‘bayanin da ake iya gane ta keɓe’) a kuma riƙe sauran don amfaniinmu a zaman bayanai mara suna (wanda yake nufi cewa bai yiwu a gane ka ba). Za mu gaya maka idan muka yi hakan. Kana iya aika mana imel a dataprotection@girleffect.org don neman a share bayananka ko idan kana da wasu tambayoyi game da bayananka.
Haka kuma kana iya nema ka karɓi wani kwafi na bayanan da muke riƙe game da kai, idan har akwai wasu a wajenmu, ko don mu gyara kowanne a cikin bayanan. Haka kuma ana kiran waɗannan Haƙƙin Samun Dama ko Haƙƙin Gyarawa. Za mu yi ƙoƙarin ba da amsa ga buƙatunka a cikin wata ɗaya da aka tabbatar da shaidarka. Sai a aika mana saƙon imel a dataprotection@girleffect.org kuma za mu aika maka wani fom da za ka cika domin mu san daidai abin da za ka so mu yi.
Ƙorarrafi.
Idan ba ka jin daɗi da yanda muke gudanar da bayananka, kana iya koda yaushe tuntuɓe mu a dataprotection@girleffect.org kuma za mu yi ƙoƙarin ba da amsa da wurwuri dai dai gwargwado, (kuma koyaushe a cikin wata ɗaya).