Madalla da ziyarci Springster! Mu ne Girl Effect kuma muna gudanar da Springster. Mu wata ƙungiyar taimako ce, a Ingila, kuma muna yin aiki wajen ƙarfafa ‘yan mata kamar ke. Ana iya samun adireshinmu da sauran bayani a ƙarƙashin waɗannan dokoki.
Sai a tabbata a karanta da kuma bi waɗannan dokoki: Ba irin dokoki da za su hana ka samun nishaɗi ba - suna nan don tabbatar da cewa an tsare kowa kuma ana yin amfani da Springster yanda ya dace!
A tuntuɓe da kowaɗane tambayoyi ko sharhohi ta hanyar saƙon imel a springster@girleffect.org. Muna son jin daga gare ka!
DOKOKIN
1). Muna iya canza waɗannan dokoki lokaci-lokaci. Sai a tabbata a farga da siga mafi kwanan nan ta dubawa nan kullum. Haka kuma muna iya canza Springster, da ya haɗa rufe shi na wucin gadi, domin a bunƙasa ƙwarewarka. Za mu yi ƙoƙarin mu sanar da kai gabannin, amma wataƙila wannan ba zai yiwuwa ba koyaushe.
2). An yi niyyan Springster don mutane tsakanin shekaru 13 – 24. Idan kana a ƙasa da shekara3, don Allah kada a yi amfani da Springster, tun da bai dace maka ba. Idan kana a ƙasa da shekara 16, don Allah tabbata a duba wajen iyayenka ko mai riƙonka kafin a yi amfani da Springster.
3). A lokacin da ana yi amfani da Springster, za mu tattara keɓaɓɓen bayani daga gare ka. Sai a karanta namu Dokar Tsare Sirri don samun:
4). Wataƙila a samu bayani game da lafiya a kan Springster. Wannan bayani bai maye gurbin shawarar kula da lafiya ba. Idan ana da wasu takamaiman tambayoyi ko damuwa game da lafiya, sai a tuntuɓi wani likita ko sauran gwanayen kula da lafiya.
5). Springster wata al’umma ce, wadda yake nufi tare da ƙunshiyar da muke saka a samu a kan Springster, mai yiwuwa ka samar da ƙunshiya ta kanka. Wannan yana iya haɗa sharhohi, bulogogi, saƙonnin twit, fodkas, taɗe-taɗe da kuma fayilolin sauti-da kuma na gani. Kafin a ba mu izini, sai a tabbata:
6). Wataƙila akwai mahaɗoɗi zuwa sauran wuraren gizo da kuma ƙungiyoyi namu a kan Springster. Waɗannan dokoki ba za mu sanya ga waɗancan wuraren gizo ba kuma ya kamata ka duba dokokin a kan kowane wurin gizo a lokacin da ake da damar zuwa wajen, tun da ba za mu iya ɗauki nauyin sauran ƙungiyoyi ba.
7) Idan an yi rajista-a zaman wani memba (ko “Springster” yanda muke so kiran ka!), za ka samu wata shigarwa da kuma kalmar sirri. Riƙe wannan bayani asiri tun da ba ka so wani dabam ya shiga Springster kuma ya nuna kamar kai! Muna fata za ka ɗauka nauyin aikin zaman memba naka.
8). Wataƙila mu nemi ra’ayinka a cikin nazarori. Sai a hallara kawai idan ana so, buƙata waɗannan nazarori ba. Muna yin wannan domin a gane mafi kyau yanda ake yi amfani da wurin gizon, da kuma don samar maka da ƙunshiya mai ƙarin amfani (da sauran masu amfani da Springster). Muna iya raba sakamakon tare da wasu, amma wannan ba zai taɓa haɗa keɓaɓɓen bayani naka sai dai an gaya mana dalla-dalla a yi amfani da shi.
9). Muna yin ƙoƙarin tabbata Springster yana da tsaron yin amfani da shi, amma ba za mu iya ba da garanti cewa bai da wasu sankarorin kwamfuta ko sirri masu lahanta ba. Ba za mu ɗauka nauyin kowane lahanta ga wayarhannu naka da wataƙila suka taso daga yin amfani da Springster.
10). Muna son a riƙe Springster da tsaro da kuma ya samu ga dukan masu amfani. Don taimaka mana, kada a yi ƙoƙarin shiga Springster ta hanya mara daidai ba, shafa dandalin da wata sankarar kwamfuta ko wani abu dabam da suke iya lahanta Spinster.
11). Sunan “Springster”, namu babban alamar shaida da kuna zanen dandaliin an mallaka su ta wajen Girl Effect. Sai a nemi izininmu kafin a yi amfani da kowane a cikin waɗannan don kowane dalili (sai dai ta yin amfani da Sprinster).
12). An samar da Springster ne don amfanin keɓe kawai. Idan kai wani kasuwanci ne, kada a yi amfani da Springster, tun da ba a yi niyya ƙunshiyarsa maka ba kuma ba ka da haƙƙoƙin yin amfani da wannan bayani.
13). Idan a kowane lokaci ka karya kowane a cikin waɗannan, mai yiwuwa (tare da sauran mataka) mu tsai da kai daga yin amfani da Springster a gaba.
14). Idan kana da wata damuwa, ko idan ka dama game da komai da ka gani a kan Springster, sai a yi magana kuma a tuntuɓe mu ta hanyar saƙon imel: springster@girleffect.org
Muna fata kana jin daɗin zama ɗaya daga cikin al’ummar Springster!!
Girl Effect wani kayyadadden kamfani ne da kuma wata ƙungiyar taimako da aka yi rajistarsa a Ingila, UK. Adireshinsa da aka rajista shi ne Ingeni Building, 17 Broadwick Street, London W1F 0AX. Lambar kamfaninsa ita ce 07516619 kuma lambar rajistar ƙungiyar taimako ita ce 1141155.