Koyon yadda za ki tsara burinki da sauran dabarun rayuwar da 'ke' kike bukata, iya bakin kokarinki
Muna koyon abubuwa da yawa masu amfani a makaranta: lissafi da kimiyya da kyakkyawan nahawu da yadda ake kulla abota, amma akwai darussan rayuwa da sai dai ki koye su a rayuwa ta yau da gobe. Wadanne dabarun sirri ne wadannan masu ban mamaki? Bari mu yi magana, yarinya.
Tsara buri
Buruka su ne tsare-tsaren da za su taimaka miki mafarkinki ya tabbata. Wadannan na iya zama abubuwan da kike son cimma idan kin kammala makaranta, ko ma lokacin da kike makarantar. Ga yadda za ki fara:
shirya bajet Daya daga cikin muhimmiyar dokar rayuwa ita ce: kar ki kashe fiye da abin da kake samu. Idan za ki fara ajiye kudi, komai kankantarsa. Idan kin yanke hukuncin sayen wani abu na nishadi, yi tunani a kan me ya sa kike bukatar wannan abun. Kada ki kuskura ki ranto kudi don ki sayi wani abu, sai har idan kina bukatarsa ko kuma wani abu ne da zai kyautata rayuwarki nan gaba, kamar fara kasuwanci ko karo karatu. Wani lokaci yadda kake kashe kudi na iya zama tarnakin cimma burinka.
Yi amfani da lokaci yadda ya kamata
Sai ki ga kamar kina da isasshen lokaci amma sam ba haka abin yake ba. Lokaci shi ne abu ma fi muhimmanci da za ki samu, don haka ki yi kyakkyawan amfani da shi. Tsara burinki, ki shirya ki kuma yi kokarin ganin cewa ba kya mu'amala da mutanen ko kum abubuwan da za su rika bata miki lokaci. Kina son kawa mai tsugudidi!
Ki rika mu'amala da mutanen kirki wadanda za su kara miki kwarin gwiwa sannan ki yi amfani da lokacinki wajen yin abubuwan da za su inganta rayuwarki!
Share your feedback