Hanyoyi guda uku da zaki yi abokan arziki na abada

Haduwa da abokai na kwarai

Abokai….ba su bane suka fi gagarumin da zamu ajiye kusa da mu?!

Wani da shekarun ku daya da zaki iya labari da, kiyi koyo da kuma ku shakata tare.

Duk muna bukatan wannan abokin ko abokiya da zamu yi dariya tare akan lokutan da muka kunyatar kan mu.

Wani da zamu iya gaya wa abubuwan da muke tunani. Wani da zai gane da mu.

Haduwa da abokai kamar haka ba karamin abu bane amma yana iya faruwa.

Kina son kiyi sabobin abokai?

Ga abubuwa guda uku da zasu taimake ki

Ki zamanto mai fara’a
Idan kina son kiyi abokai kina bukatan ki zama maifara’a. ki nuna sha’awa a wasu mutane. Mutane na son suyi abokai da wani dake son murmushi kuma nuna yana musu so.

Kada ki canza kanki
Zaki samu abokan arziki idan kika nuna asalin kanki. Ba lalai bane sai kinyi magana, ko tafiya ko saka kaya a wani takamammen hanya. Ki bari mutane su so ki dan asalin ki. Kada ki gwada wayencewa ki zama wani da ba ke ba.

KIje yanar gizo gizo
Kina kasa samun abokai a al’ummar ku? KIje yanar gizo gizo. Zaki iya haduwa da yan mata kamar irin ki a nan GEM. Zaki iya abokantaka da yan mata daga duk fadin duniya. Ko ki gwada samun kungiyar yan mata a facebook da suke da irin tunani kamar ki.

Ki tuna ki tsirata kanki idan kina kan layi. Kada ki hadu da su ke daya a waje.

Kada ki bawa wani da baki sani ba kowane mallakin bayanin ki na sirri.

kina kasa samun abokai? Kina ji kamar baki kusa da abokiyar ki yanzu? Kiyi mana magana a shafin sharhin mu.

Share your feedback