Yadda zaki karfafa gwiwan ki
Wannan Litinin shine farawan aikin na mako mu a makaranta.
Shugaban makarantan mu tace tilas ne kowa ya dauke wani aji na horas da kwarewa saboda mu koya wani kwarewa.
Bayan wata daya, zamu yi wani babban shiri da mutane zasu zo su kalle mu muna nuna sabobin kwarewar me. Shugaban makarnatan ta gaya mana wanda suka zo farko a kowane aji zasu samu kyauta.
Bayan da muka bar taron, a guje naje wajan allon sanarwa domin na duba sunayen kungiyoyin. Naga: na yin aiki a lambu, da na yin abin sha, dana horon kwanfuta, da kuma na koyan yin takalmi.
A lokacin wasan mu, shugaban makarantan mu tazo ajin mu ta gaya mana akan dukka ajin horaswa na kwarewa.
AIKIN LAMBU
A wannan ajin zamu koya yadda zamu shuka fure kamar wardi da furannin. Shugaban makarantan mu tace zamu kara koya yadda zamu kyawata muhallin mu. Dalibai a wannan ajin zasu iya samun kudi daga siyar da fure, da shuki harda ya yan itatuwa da suka shuka.
YIN ABUN SHA
A wannan ajin zamu koya yin abun sha kamar zobo, da kunu, da kuma abun sha da aka yi daga lemun tsami. Zamu kara koya yadda zamu tattara abun shan. Yan mata zasu koya yadda zasu kafa da kuma bi da sana’ar. Tace a nan zamu iya yin abun sha da zamu siyar da a al’ummar mu.
HORASWA NA KWAMFUTA
A nan za’a koya mana yadda zamu yi amfani da kwamfuta. Za’a koya mana yadda zamu yi amfani da Microsoft word.
Shugaban makarantan tace da kwarewa kamar haka zamu iya daukan aikin bugun tafireta. Zamu iya fara kasuwanci kwamfuta a rayuwar mu na nan gaba.
YIN TAKALMI
Shugaban makarantan mu tace za’a koya mana yadda zamu yi takalmin makaranta. Zasu koya mana yadda zamu fara kasuwancin takalmi. Yadda zamu taffiyad da kasuwancin? Gaskiya na ji dadi akan ajin koyan talkamin. Yanzu zan iya yin silifas da takalmin makaranta.
Bayan da ta gama, shugaban makarantan mu tace dukka wadannan ajin nada muhimmanci. Zai iya taimakon mu fara namu sana’ar ko kuwa ya taimake mu yin kudi yanzu harda lokacin da mukayi girma.
Share your feedback