HANYOYI GUDA BIYAR DA ZASU TAIMAKE KI JAN KUSA DA MURADIN KI

Jan kusa da buri na

Kina son ki zama mai inganci?

Kina son kici wani jarabawa, ko ki gama wannan makarantar koyon hoto, ko kina son ki zama likita, kwarerran dan wasa,ko matukin jirgin sama, ko kuwa madinki?

kina son ki zama mace na farko mai gyara kayan lantarki a al’ummar ku?

Kina son ki zama mace na farko da ta zama shugaban kasa a Naijeria?

Koda menene burin ki, zaki iya cin nasara.

Zai dauki mayar da hankali, horaswa da karin aiki sosai, amma mai yiwuwa ne.

Ga wasu matakin da zaki bi da zai taimake ki jawo kusa da burin.

Ki gan shi
Ki hango kanki kina yin rayuwa a yadda kike so. Na san kina murmushi da kike yin tunanin.

Kiyi imani da kanki
Yanzu da kike gani, dole ki imani da shi. Kina bukatan tabacci da burin ki. Kada ki yarda wani ya gaya miki baza ki iya cin nasara ba.

Rubuta shi
Ki rubuta shi ko kuwa ki ja zane a wani littafi na musamman.
Ko kuwa ki rubuta ko ki ja zane ki manne shi a bangon dakin ki. Zaki iya kara hotuna daga mujalla ko takarda daya shafe burin ki.
Ki kalli abun da kika rubuta/ko kika ja zane kowane rana. Zai tuna miki da abun da kike aiki ma.

Ki fara aiki akan sa
Kada ki zauna a wajan ki tsammanin zasu fado miki a cinya ba. Akwai kwarewa da kike bukata domin ki bunkasa burin ki? Kina butakan horaswa ko karin ilmi? Ki nema abun da kike bukata. Ki fara aiki zuwa gare sa.

Ki samu mai shawarta
Akwai wani mai yin abun da kike son kiyi?
Ki samo komai akan su.

Ki koya dukka matakin da suka dauka domin su kai inda suke yanzu. Sa’a nan kema zaki iya daukawa.

Ba sai kin san su ba. Zaki iya karatu game da su a ranar gizo gizo ko a mujalla.

Idan mutumin wani ne da kika sani, ki tambaye su ko zasu shawarta ki.

Bai isa ace ki zauna ki ta babban tunani ba.

Yakamata kina mayar da hankali, da horaswa, da yin kafiya, da kuma karin aiki.

Me kike so ki cimma nasara? Wanda mataki kike dauka domin ki ci nasara? ki gaya mana a shafin sharhin mu.

Share your feedback