Ga Hanyoyi guda biyar yadda zaki canza lokacin wasan ki zuwa riba

Yau safga ne, gobe zai iya zama sana’an ki.

Akwai abun da kika iya yi sosai?

koda rubutu ne, ko zane zane, ko daukan kyawawan hotuna, ko abinci, ko gyaran gashi, ko dinki, ko kuma yin magana, zaki iya mai da shi sana’a.

kina son ki san yadda zaki yi? cigaba da karanta.

Ki fara da abunda kike kauna
Menene abun nan da kike son yi? samun kasuwanci zai iya zama abu mai wuya wasu lokaci. Amma yin abun da kike so zai sa taurin aikin ya zama mai sauki.

Ki saka kanki ingantuwa
Ki gwaji har sai kin kware. Ki samu mutane dake yin abun da kike son kiyi. Zasu iya zama tsaranki, ko wani daya girme ki, ko wani sananne.Ki gano yadda suka fara sai ki dauke darussa daga labarin su. ki nemo karin bayani daga takaddu ko a shafin yanar gizo gizo. Ki cigaba da koya har sai kin ingantuwa.

Ki nemo kasuwancin ki
Wa kika sanni da zai iya amfani da kwarewar ki? Ki tambaye iyalai ki ko abokan ki ko sun san wani da zai biyan ki. Kiyi magana da wadannan mutanen akan abun da suke bukata da kuma nawa zasu biya ki.

Ki gaya wa mutane akan shi
Da zaran kin yanke shawara cewa kin shriya, kada kiji kunya. Ki gaya wa iyalai ki, da abokan ki, da yan ajin ku a makaranta, harda yan farfajiyar gidan ku. Zasu iya zama abokan kasuwancin ki na farko. idan suka ji dadin aikin ki zasu gaya wa wasu mutune. Idan kina samun abokan kasuwanci sosai sai ki gaya musu su fada wa sauran abokan su da iyalai su.

Ki ririta kudaden ki
Ki ajiye bayanan kudaden da kike samu da wanda kike kashe. Kin fara kasuwanci saboda ki samu kudi ma kanki, amma kada ki kashe duka. ki ajiye wasu dan ki siya kayan aiki dan ki inganta kasuwancin ki.

Ki tuna ki tsirata kanki! Idan zaki je gidan mutane ko ofishi, kada kije ke daya. Idan suka zo gidan ki, ki tabata kina da wani ko wata da kika yarda da anan. Kada ki ajiye kudade da yawa da ke. Ki tambaye wani babba da kika yarda da akan bude asusun ajiya na banki.

Safgan ki zai iya bude miki kofofin alheri. Sai ki bunkasa kani dan kici nasara a sana’an ki. Kina da safga da zai iya kawo miki kudi? Ki gaya mana a shafin sharhin mu.

Share your feedback