Yin aiki zuwa rayuwa na nan gaba mai kyau
Wata rana mahaifiyata ta tambaye ni mai nake so na zama nan gaba. Na gaya mata ban sani ba. Na gaya mata na kankanta, zan tunanin sa nan gaba. Ta gaya mun na zauna. Sai ta gaya mun abun da nayi yanzu zai shafe ni anjima idan nayi girma. Na tambaye ta “A ta yaya?” Ta kira sunayen wasu tsofofi a unguwar mu. Ta tambaye ni wanda ya shirya rayuwar sa da wanda bai shirya ba. Shine na gane. Wanda suke fama basu shirya da kyau ba.
Tace idan ina son na ji dadin rayuwa ta na gaba, akwai wasu abubuwan da zan iya yi yau. Ina son na raba da ku, domin ku abokai na ne.
Maida hankali akan yau
Tace kowane rana na rubuta abubuwan daya kamata nayi. Idan ina yi, na ringa jan maki. A haka, zan tabata nayi komai. Ta kara cewa na kara kokari kowane rana, a dukka abun da zan yi.
Setin Muradi
Tace na rubuta abun da nake son nayi a nan gaba. Sai na rubuta yadda zan ci burin su. Tace na rubuta abubuwa guda ishirin da zan iya yi da kuma wanda bazan iya yi ba. Abubuwan da nake son nayi kuma na san zan yi da kyau.
Yin karatu sosai
Tace abun da zanyi daga nan shine na kula da aikin makarnata. Saboda idan babu ilmi, bazan san dukka abubuwan da nake bukata domin cin buri na.
Tare ko ajiye kudi
Tace na daina kashe kowane kudi daya shiga hannu na. Tace na ringa ajiye kudi na. Ta hanyar nan, ina dashi idan ina bukatan sa a nan gaba
Zabi abokan kwarai
Tace na kiyaye da mutanen da nake kira abokai na. Tace idan na ajiye abokai mara kyau bazan ci buri na ba. Abokan arziki zasu taimake ni idan ina butakan su.
Menene wasu abubuwan da zaki iya yi dan samun rayuwa mai kyau nan gaba? Gaya mana a shafin sharhin mu.
Share your feedback