Matakai domin samun rayuwa na nan gaba mafi inganci

Duk abun da muke so a rayuwa na nan gaba na faruwa tun yanzu.

Kina son ki zama mace mai kasuwanci, ko likita, ko lauya, ko wanda take kula da harkan kudade, ko mawakiya, ko kuwa injiniya? Ya kamata ki fara tsara abun da zaki yi tun yanzu.

Idan ana son kowane gini ya tsaya da karfi ya kamata yana da tushe mai karfi. Idan kina son ki samu nasara a rayuwa, kina bukatan shiri da kyau.

Ga wasu siddabaru da zai taimake ki;

  1. Rubuta abun da kike son ki zama a nan gaba. Ko kuwa zaki iya rubuta abubuwan da kike son yi. Kiyi tunanin ayyuka dake dangantaka da abubuwan da kike son yi. Ga misali, idan kina son rubutu toh zaki iya rubuta shi a kasa- mai rubuce rubuce, yar jarida, mai yin bincike, ko kuwa mai koyarwa, da sauran su. Idan kika kasa tunanin kowane aiki dake dangantaka da abubuwan da kike son yi, ki tambaye wata abokiyar ki da kika yarda da ko kuwa wani baligin mutum su baki shawara.
  2. Sai kiyi tunanin ayyukan da aka jera da zaki so kiyi a kowane rana. Kiyi magana da mutane dake aikin nan.
  3. Kiyi bincike akan farashin dake dangantaka da burin ki. Ga misali, wasu ayyuka na bukatan wani kwarewa na musamman. Ya kamata ki san nawa ne farashin aikin da kike nema da kuma tsawon lokacin.
  4. Ki cigaba da kola da mutane dake da aikin da kike so. Kiyi magana da mutane dake al’ummar ki, ki karanta takardu da kuma makala akan mutane dake da aikin nan. Idan zaki iya, kije taro da zai iya baki bayani akan mutane dake yin aikin nan kowane rana kuma dalilin daya sa suke yin sa.
  5. Ki koya yadda zaki tsara da kuma karya burin ki zuwa yan kankanin aiki. Ga misali, idan kina son ki ci karshen jarabawan ki a darasin adabi domin ki ki zama yar jarida, toh ya kamata ki samu dabara na wata-wata a yadda zaki yi karatu kuma ki karanta takardu domin ki ci nasaran burin ki. Idan kina son ki zama shugaba a al’ummar ki, kiyi wani abu a kowane wata dake koyarwa akan shugabanci.
  6. Kada ki daina koyo. Yanar gizo gizo ya kara saka samun bayanai sauki. Ki nema shafin yanar gizo gizo kamar ehow.com da kuma hoton bidiyo a youtube da zai baki aji a kyauta akan kusan komai.

Muna son mu san abun da kike yi domin shirya rayuwar ki na nan gaba.

Gaya mana a shafin sharhi.

Share your feedback