Na kasa samun aiki

Ga abubuwa guda biyar da zai taimake ku samun aikin yi

Kasancewa ba tare da tushen samun kudi ba nada wuya, musamman idan kuna da mutane dake dogara da ku.

A yanzu mai yiwuwa baku makaranta kuma kuna neman abun yi. Kuma duk tunanin ku ya kasance a yadda zaku samu kudi.

Eh baku fara samun kudi ba, amma akwai sauran abubuwa da zaku iya yi kafan nan.

Abubuwa da zasu dauka muku lokaci kuma su taimake ku a rayuwar ku na gaba.

Abubuwa kamar jeri guda biyar na nan kasa:

  • Ku saka kai a wani kungiya a al’ummar ku. Ku bada sa’o’i kadan ko ranaku a mako domin ku dan samu lokacin neman aiki. Aikin sa kai na iya jawo damar samun aiki kuma zaku iya samun kwarewar aiki. Kuma akwai wani alfahari da ake ji idan aka taimake mutane.
  • Motsa jiki! Yin wasannin motsa jiki zai kara saka ku jin dadi. Ku shiga ko kuwa ku fara wani ajin wasanin motsa jiki ko kuwa wani kungiya wasanin motsa jiki a ungwan ku. Hanya ne mai kyau na haduwa da mutane (mai yiwuwa daya daga cikin su ya taimake ku)
  • Kuyi nomar sa, ku girka sa. Kuna da dan fili a kusa daku? Ku fara wani lambun ganye. Wannan ba zai baku aikin yi ba kadai amma zaku iya samun kudi daga siyar da abun da kuka noma. Maraba da zuwa sana’a!
  • Ku dauki wani aji. Ku nema wani makaranta mai arha. Koyar wani sabon kwarewa zai taimakon ku kara girma kuma hanya ne mai kyau da zaku samu kudi.
  • Ku samu shawara. Kuyi wa wata mai irin kasuwancin da kuke son yi magana. Ku tambaye su ko zaku iya zuwa kwashe lokaci a wajan aikin su na rana daya domin ku ga yadda suke aiki. Hanya ne mai kyau da zaku sani idan aikin da kuke so zai dace da ku.

Ku cire hankalin a kan neman aiki na minti daya. Kuji dadin rayuwa ku a yayin da kuke gwada sauran abubuwa.

Amma ku kula da sabobin mutane da kuke haduwa da. Musamman idan suka yi saurin yin muku alkawarin samun aiki ko kudi ta wani hanya mara kyau.

Wanne sauran aiki masu riba ne kuke ganin zaku iya yi domin samun abun yi? Ku rarraba damu a wajan sharhi.

Share your feedback