Ba koda yaushe ba! Dabaru akan yadda zaku samu abun da kuke kauna kuma kuci nasara.
Idan kuna son kuci nasara yakamata ku shirya yin koyi da kuma yin aiki sosai domin kara inganta kwarewar ku.
Amma ba lallai bane sai yin koyi ya kasance a makaranta kawai, zai iya faruwa a wani cibiyar sana’a, ta darasi, da kuma rayuwa da kwarewa. Ba lallai sai ya kasance a makaranta ba.
Idan kuna son kuci nasara kuna bukatan yin aiki sosai.
A nan kasa zaku samu wasu abubuwa da zaku iya yi
Ku nemo wani abun da kuke so sai kuyi sa
Kuna son yin kitso, ko yin huluna, ko kuwa dutsen ado? Kuna son gyara kayan lantarki? Kuna son yin rubutu? Ku nemo wani abu da kuke son yi sai ku fara yin sa. Ku samu wani horo akan sa. Zaku iya samun horaswa daga wani amintaccen mutum dake aikin nan a al’ummar ku.
Ku samu horaswa
Ku zama kwarerru ta samun horaswa. Zaku iya yin rijista ku zama dalibai. Kuna son ku gyara motoci? Ku zama dalibai a shagon wani makaniki. Bari su koya muku abun da kuke bukatan kwarewa da.
Ku koyar da kanku
Akwai abububwa da yawa da zaku iya koya a shafin yanar gizo. Kuna son ku koya yadda zaku zama mai dafa abinci? Ku duba nan. Ku karanta akan sa a shafin yanar gizo gizo. Ku koyar da kanku.
Ku samu mai shawarta
Ku nemo wani dake da kwarewa a aikin ku. Ku koya daga wajan su kai tsaye ko a kaikaice. Ku karanta akan su. Ku tambaye su su nuna muku yadda suka samu suka ci nasara.
Kuyi imani cewa zaku ci nasara
Yana daukan yin imani da kanku. Ko da kwarewa mafi kyau a gaba dayan duniya idan baku yi imani da kanku cewa zaku cimma burin ku ba, mai yiwuwa baza ku yi sa da kyau ba.
Eh zaku iya cin nasara idan kuka je makaranta amma idan baza ku iya zuwa makaranta ba, akwai sauran hanyoyi da zaku iya samun nasara.
Baku makaranta yanzu? Gaya mana abu daya da kuke yi domin ku bunkasa kanku
Share your feedback