Abun da zaku iya yi da kanku: Kuyi naku allon muradi

Kuyi nishadi da kuma fasaha da burin ku

Kowa nada muradi na rayuwar sa na gaba. Hanya daya da zamu iya cimma wadannan burin shine idan muka kirkira wani allon muradi.

Allon muradi wani kayan aiki ne ko wani abu da zaku iya amfani domin ku tunatar da kanku akan burin ku ko wahayi.

Wannan allon zai taimaka kirkira wani hoton abun da kuke son ku cimma. Wannan allon zai iya saka muradin ku zama na hakika kuma ku cimma burin ku.

Amma kafan ku kirkira shi, yana da muhimmanci ku tabbatar da burin ku. Ana nufin kun san ko menene, kun san abun da kuke so ku cimma da kuma yadda kuke son rayuwar ku na gaba ya kasance.

Kuna al’ajabin yadda zaku kirkira wannan allon muradin? Toh, mu fara;

Abun da kuke bukata

  1. Fallen takadar kwali
  2. Ku samu almakshi
  3. Gam
  4. Tsohon jarida ko mujalla

Abun da zaku yi

  1. Ku duba mujallar sai ku zabi hotuna daya dace da rayuwar ku na gaba da kuke tunani. Wannan zai iya zama hotunan mutane dake yin muku wahayi, wani mota da kuke sha’awa, wajaje da zaku so ku ziyarta, abubuwa da kuke son yi, ko kuwa aikin nan da kuke fatan samuwa. Allon muradin ku sirrin ku ne, saboda haka babu hoton daya dace da wanda bai dace ba. Kuyi tunani da kyau kuma ku tabbata kunyi nishadi.
  2. Ku yanke kowane hoto daya muku wahayi sai ku manne su a fallen takardar kwallin ku.
  3. Ku nemo ko kuwa ku rubuta wasu kwaito masu karfafa gwiwa sai ku manne su a fallen takardar kwallin.
  4. Sai idan kuka gama, ku manne allon muradin ku a wani waje da zaku riga gani kowane rana, kamar bangon dakin ku ko a kan kofa domin ku tunatar da kanku akan burin ku.

Lokaci ya kai da zaku fara.

Dukkan mu nada muradi na rayuwar mu na gaba amma baza su auku ba da kan su.

Muna bukatan yin aiki sosai.

Allon muradin zai taimake mu kasancewa da tunani mai karfafa gwiwa kuma ya tunatar damu kada mu fid da rai idan abubuwa suka kasance da wuya.

Ku gwada wannan sai ku tura hotunan allon muradin ku zuwa shafin Facebook din mu.

Share your feedback