Jerin abubuwa da zaku iya yi: Littafin rubutu na atamfa

Ku juya wani tsohon abu zuwa wani sabon abu

Idan kuna da wani littafi da kuke amfani a kowane lokaci, mai yiwuwa kuso ku canza masa kamani.

Akwai abubuwa da yawa da zaku iya amfani domin kuyi wannan. Daya daga cikin wadannan abubuwan shine atamfa.

Dukkan mu nason kayan atamfa shiyasa muke son muyi amfani da shi. Zaku iya amfani da tsohon mayafi ko kuwa ku tambaye wani tela ya baku kyallen atamfa da basu amfani da.

Zaku iya amfani da wani kyalle da kuke da a gida.

Kuma idan kuna da isasshen littafai da kyalle a gida da zaku iya yin fiye da daya fa? Iyalan ku da abokan ku zasu so su siyo wadannan takardun masu kyau daga wajan ku. Ra’ayin kasuwanci mai kyau!

Ga abubuwan da kuke bukata;

  1. Atamfa ko kuwa wani kyalle
  2. Almakashi
  3. Gam
  4. Wani littafi
note_eng_1.jpg

Yadda zaku yi sa

  • Ku bude murfin littafin sai ku saka shi a kan kyallen.
note_engl2.jpg
  • Kuyi amfani da almakashin ku yanke tsakiyar kyallen saboda ya ninka a tsakiyar littafin kamar yadda aka nuna a hoton kasa.
notebook_engl3.jpg
  • Ku saka gam a gaba dayan kyallen saboda ya manne da littafin. Ku saka gam din a bayan littafin( gaba da baya).
notebook_eng_4.jpg notebok_english_5.jpg
  • Ku latsa kyallen saboda ya manne da gaba da bayan littafin.
notebook_enlgish_6.jpg
  • Ku saka gam din a cikin murfin littafin. Kada ku shafa gam din a ko ina. Kawai a bakin murfin saboda kyallen ya manne idan kuka ninka shi ya ciki.
notebook_7.jpg
  • Ku ninka kyallen kamar yadda kuka gani a nan kasa saboda ya manne da littafin a wajan da kuka saka gam din.
note8.jpg note_9.jpg
  • Kuyi dukka wannan wa murfin gaba da kuma murfin bayan littafin.
  • Kun tuna wannan yankan da kuka yi a farko? Toh ku sanke shi a tsakiyar littafin. Zaku iya manne shi da gam ko kuwa ku cusa shi cikin wayar littafin idan yana dashi.
notebook_english_10.jpg
  • Ku yanke murraba’ai biyu daga fallen littafin, ku tabbata bakin ya mike. Ku saka musu gam, sai ku manne su da baya da gaban littafin. Wannan zai rufe bakin kyallen domin ya kara saka shi kyau.
notebook_11.jpg notebook12.jpg
  • Ku bar gam din ya bushe na sa’o’i kadan. Shikenan kun shirya amfani da littafin ku.
notebook_english_13.jpg notebook_english_14.jpg

Zaku iya samun kudi da wannan. Abokai da mutane kusa daku zasu iya baku tsofofin atamfar su da littafan su domin kuyi musu wannan littafin mai kyau. Zaku iya cajin su kudi kadan na yin wannan.

Me kuke tunani akan wannan aikin? Akwai wani abu kuma da kuke son muyi? Gaya mana a wajan sharhi.

Share your feedback