Jerin abubuwa da zaku iya yi da kanku: Abun kama gashi

Yadda zaku kama gashin ku da kyau kuma ku gyara shi

Kun san me zaku kirkira da wani tsohon safa? Abun kama gashin!

Eh, da gaske.

Lokaci ya kai da zaku yi ban kwana da roba sai kuyi maraba da wannan abun kama gashin.

Kuma yin sa bai da wuya.

Hakika zaku iya samun kudi daga siyar da shi wa abokan ku, iyalin ku, ko kuwa wa yan mata a al’ummar ku.

Toh yanzu, mu fara.

Abubuwan da kuke bukata

- Safa biyu (sabo ko tsoho)

- Almakashi

R1.jpg

Mataki na daya: Ku yanke saman safar

R2.jpg

Idan kuka gama zai yi kama da hoton nan kasa.

R3.jpg

Mataki na biyu Ku yanke gefen yatsar kafa.

R4.jpg

Mataki na uku: Ku nannade safar da hankali

R6.jpg R7.jpg

Idan kuka gama zai yi kama dana hoton nan na kasa

R7_peeXjtg.jpg

Kuma zaku iya amfani da samar da kuka yanke ku kama gashin ku

R8.jpg

Toh shikenan mun gama. Lokaci ya kai ayi ado……

R9.jpg

Zaku iya amfani dashi a kan kitson gashin doki

R10.jpg

Ku gan sa a kan kitson zane

R11.jpg

Kuma zaku iya amfani dashi ku kama gashin ku.

Kuje ku gwada sai ku gaya mana yadda ya kasance a sashin sharhi.

Share your feedback