erin abubuwa da zaku iya yi da kanku: Abun goge takalmi mai ruwa

Domin samun wannan walkiyar

Idan zaku je makaranta, ko gidan yan uwan ku, ko kuwa wani taro, me kuke yawan dubuwa?

Tsaftar gashi da kuma tsarin gashi?

Tsaftar kaya?

Tsaftar yatsu?

Takalman ku fa, kuna tabbata cewa suna da tsafta da kuma walkiya?

Idan kuka ce eh, toh wannan aikin naku ne.

Zaku so wannan abun goge takalmin. Yana da saukin yi kuma kuna bukatan abubuwa guda uku ne kawai domin kuyi sa.

Idan abokan ku suka ga yadda takalman ku ke walkiya, mai yiwuwa zaku iya siyar musu ko kuwa ku fara wani ajin koyarwa a kyauta.

Abun da kuke bikata

  1. Lemun tsami daya
  2. Man zaitun
  3. Wani karamin kwano mai murfi.
image1_z7AAr0y.jpg

Yadda zaku yi sa

Mataki daya
Ku matse dukkan ruwa daga lemun.

image6.jpg

Mataki na biyu
Ku cire dukkan irin shuka da kuma sauran datti daga ruwan lemun.

image9.jpg

Mataki na uku
Kuyi amfani da murfin kwalban man zaitun ku ku auna ruwan lemun so biyu. Ko kuwa zaku iya auna cokali biyu na ruwan lemun. Ku saka shi a karamin kwanan ku mai tsafta.

image8.jpg

Mataki na hudu
Kuyi amfani da murfin man zaitun ku ku auna man zaitun so biyu. Ko kuwa zaku iya amfani da cokali ku auna so hudu. Ku hada shi da ruwan lemun dake cikin kwanan.

image7.jpg

Mataki na biyar
Ku hada ruwan lemun da man zaitun sai ku juya shi sosai.

image10.jpg

Shikenan!!!

image12.jpg image13.jpg

Yadda zaku yi amfani

Mataki na daya
Ku tsoma wani kyale mai tsafta a cikin abun goge takalmin. Sai ku bar takalmin na minti kadan.

image3.jpg

Mataki na biyu
Kuyi amfani da tsummar ku goge takalmin (wannan yana nufin cewa goge shi da takalmin da karfi saboda yayi kyalli da kyau)

image11.jpg

Ga takalmin kafan a goge….

image4.jpg

Sai kuma gashi nan bayan da aka goge…

image2.jpg

Abubuwa da yakamata ku tuna

  • Kuyi amfani da abun goge takalmin a takalmin dake da tsafta. mj
  • Kada kuyi amfani da wannnan abun goge takalmin a takalmin fata. Idan kuka yi zai yi datti dashi. Zaku iya amfani dashi a kowane irin launin takalmin.
  • Wannan abun goge takalmin zai iya dadewa har zuwa mako daya idan baku ajiyar sa a firji ba. Zai iya dadewa har zuwa wata daya a firji.

Zaku gwada wannan abun goge takalmin? Ku rarraba damu a sashin sharhi.

Share your feedback