Jerin abubuwa da zaku iya yi da kanku: Jakan riga

Ku rike sa kuyi yanga

Dukkan mu na amfani da jaka domin abubuwa da yawa. Muna amfani dashi a kasuwa, a makaranta, idan zamu je ungwa da kuma sauran lamurra.

Baza ku so ku san yadda zaku iya yin naku jakan ba?

Zaku iya amfani dasu ko kuwa ku siyar da su wa abokan ku da makwaftar ku.

Kuma zaku yi nishadin yin wani sabon abu!

Ga hanya daya da zaku iya yin naku jaka. Aiki ne da zaku iya yi da kanku ko kuwa tare da abokan ku.

Abun da kuke bukata

  1. Tsohon riga ( Riga mai kauri zai fi kyaun yin jaka)
  2. Almakashi
1_Vd6r0Db.jpg

Yadda zaku yi sa

Mataki na daya
Ku yanke wuyar da hannun rigar kamar yadda aka nuna a hoton nan kasa.

2_OLZKQvg.jpg

Mataki na biyu
Ku yanke kasar rigar kamar yadda aka nuna a hoton a nan kasa. Ku zagaye kasar rigar da yankin.

3_JzzYYRU.jpg

Idan kuka gama kamanin kasar riga zai yi kamar wannan….

4.jpg

Mataki na uku
Ku kama kasar bayan rigar da na gaban rigar sai ku daura su tare. Ku tabbata cewa kunyi sa da karfi.

Shikenan kun gama!

4B_v9IRa0q.jpg 5_9JFcfqC.jpg

Zaku iya saka abubuwa a jakar ku kamar takardu. Kuma zaku iya yin masa ado duk yadda kuke so. Zaku iya masa fenti da launi ko kuwa kuyi masa zane da alkalami mai launi.

6.jpg

A karshe, zaku iya juya ciki jakan zuwa waje domin ku basa wani kamani dabam.

7.jpg final_bag.jpg

Ku gaya mana a sashin sharhi idan kuma zaku yi naku jakan. Muna so mu san yadda kuka yi!

Ku sake ku rarraba hotunan naku jakar rigar a shafin Facebook din mu.

Share your feedback