Ki kamala abun da kika fara

Ki nemo yadda zaki samu daman gama abubuwa a mataki daya a lokaci daya!

Kece kullun na karshen yin abu?

Kina son jira sai a karshen minti kafan ki fara yin abu?

Idan zuciyar ki na ihun “E”! toh ke mai dakatad da abu ne.

Yana nufi cewa kina son bata lokaci sai abu yayi lati.

Ba lalai sai kin zama yarinya mai karfi kafan ki samu yin abubuwa a lokacin daya kamata.

Abun da kike bukata shine wasu Siddabaru kamar na nan kasa da zasu taimake ki.

Ki samu takarda da alkalami
Ki samu littafi, wanda zaki iya daukawa a kowane waje kowane rana. Ki rubuta abun da kike bukatan tunawa. Ki tabata kina nan dashi a kusa dake a kowane lokaci.


Ki kirkira abubuwan daya kamata kiyi a jere.
Dukkan mu na bukatan abun da zamu ajiye a shirye. A kan jerin abubuwan da zaki yi, ki rubuta abubuwan da kike bukatan yi. Ki rubuta su a yanayin mafi muhimmanci. Ki rubuta lokacin da kike son ki fara. Da kuma lokacin da kike son ki kammala. A wannan hanyar, zaki san abun daya kamata kiyi kuma zaki iya yi da sauri.

Ki bawa kanki lada
Duk lokacin da kika yi wani abu daga jerin abubuwan daya kamata kiyi zaki iya bawa kanki sakayya. Misali. Idan kika gama wankin tufafin ki kafan karfe uku na rana, zaki iya yanke shawara ko kallon talabijin na minti goma sha biyar a matsayin lada.

Ki guje shagaltarwa
Shagaltarwa na hana ki samun yin abubuwa. Ki ajiye wayan nan, ki kasha talabijin sai ki maida hankali a abubuwan daya kamata kiyi. Kiyi bankwana da tashan talabijin nan na wakoki da kuma na telemundo har sai kin kammala aikin ki. Kada ki bari wani abu ko wani ya shagaltar da ke.

Shawarar mu mai sauki ne “ki kammala kowane abu kafan ki far”.

Kina samun matsaloli a kammala aikin ki? Kina tsayawa a rabin hanya? Kin samu hanyar da zaki tabata baki shagaltar daga Muradin ki? Koda menene kiyi mana magana a shafin sharhin mu.

Share your feedback