Matakai guda biyar akan yin magana

Muryan ku nada muhimmanci

Kun taba ji kamar ba’a sauraran ku?

Mai yiwuwa babban abokiyar ku bata amince da wani abu da kuka tsara zakuyi ba. Ko kuwa iyayen ku na son ku zama likita a maimakon mai wasan kwaikwayo. Dukkan wannan ya dan saka ku yn takaici, ko?

Gaskiyar shine, yana da kyau kuyi magana, ku tabbata cewa anji ku. Idan baku san yadda zaku bi dashi ba, wadannan dabarun zasu taimake ku:

Ku amince da Ilhamar ku
Koda yaushe ku saurara wannan karamar muryan nan na cikin kan ku. Idan wani abu da wani ya fadi ko kuwa ya aikata bai zauna muku da kyau ba, toh mai yiwuwa bai da kyau.

Ku samu tabbaci amma da girmamawa
Idan kuna magana, kuyi amfani da murya mai hankali. Idan kuna jin takaici, ku bar wajan na lokaci kadan. Wannan zai taimake ku yin tunanin abun da kuke son ku fadi.

Ku saurara dayan mutumin
Mai yiwuwa dayan mutumin nada ra’ayi dabam, amma suma suna da iko da za’a aji su. Sauraran su zai taimake ku gane hanyoyi dabam da mutane ke tunani. Ba lallai sai mun yarda da komai ba, kuma babu matsala da wannan.

Ku mallake shi
Kuyi amfani da kalmar “Ni” a farkon maganar ku. Ga misali, ku ce “Naji kamar bai daice kiyi mun magana haka ba” a maimakon “ Me ke damun ki? Kada ki sake mun magana haka”. Mutane sunfi maida martani da kyau idan ba’a musu farmaki ba.

Ku bayyana kanku
Ku rarraba tunanin ku da kuma ra’ayin ku a hankali. Ga misali, idan babban abokiyar ku na son ta buga ludo a yayin da kuke son ku yi wasan kati, kuyi musu magana da hankali kuma da girmamawa.

Share your feedback