Cin jarabawa a makaranta

Dukka wannan ya danganta da yin aiki sosai

Daya daga cikin abubuwan dana koya a matsayin dalibi shine cewa kowa nada karfi. Wasu mutane nada hikiman kalmomi da kuma yin karatu shiyasa suke samun maki mai kyau a darasin turanci. Wasu mutane kuma nada hikima a yin abubuwa da hannun su shiyasa suke son darussa kamar ilmin tattalin arziki da kuma ilmin fasahar zane.

Ni kuma, daliba ce mai kokari amma ina da matsala daya - ilmin lissafi. Ina son na ci dukka jarabawa na amma na kasa cin wannan. Na cigaba da fadiwa kuma yana saka ni bakin ciki. Kamar, kuyi tunanin yadda zaku ji idan kuka je gida kuka nuna wa iyayen ku cewa kun sake fadiwa kuma!

Shiyasa na yanke shawara cewa dole sai na canza wannan al’ammarin zuwa cin nasara. Kuma ina son na ci nasara a wannan darasin domin na nuna cewa yan mata ma zasu iya yin ilmin lissafi. Yan maza na yi kamar su kadai ne zasu iya yin ilmin lissafi kuma ban yarda ba.

Me nayi? Na samu mutane da suka iya lissafi sosai da kuma zasu yarda su koya mun. Wadannan mutanen suka zama abokai na kuma har suna son na ci nasara fiye da nake so wa kaina! Abokan arziki sune mafi kyau!

Sunyi mun kokari kuma ni ma nayi kokari. Muka tsara wani ajin darasi da zai taimake ni kara gane darasin kafan na dauke jarabawana na karshe.

Ya jarabawan ya kasance? Toh, na kara yin kokari, amma banyi sosai ba a ilmin lissafi kamar sauran darussan. A gaskiya, dukka karatun nan ya taimake ni yin fiye dana saba a darussan dana fi so.

Abu mafi muhimmancin shine sakamako na ya saka ni samun shigar jami’a na karanta darasin da nake so. Nayi murna dana yi aiki sosai kuma nayi iyan kokarina na fahimce ilmin lissafi, amma kuma nayi farin ciki da ban tilasta kaina na dauke wani darasin jami’a dake bukatan lissafin ilmi bayan ina da sauran kwarewa masu kyau.

Abu mafi kyau shine masu koyar dani sun cigaba da zama abokai na yau. Daya daga cikin su, Helen na son ta karanta ilmin lissafi da injiniya idan ta je jami’a. Toh, wa yace ilmin lissafi na yan maza ne kawai!

Kuna da darussa da kuke son sosai da kuma wasu da baku so? Yawancin mutane nada, ku gaya mana akan sa a sashin sharhi.

Share your feedback