Karamar darasi zai iya taimakon ku a rayuwa
Yawancin mu na sha’awar yayin mu. Yan uwa mata ko maza– harda wasu yan dangi! Muna sha’awar su sosai. Muna son mu zama kamar su idan muka yi girma.
Amma ba sai mun jira har sai mun kai shekarun su ba. Zamu iya koya abu daya ko biyu daga wajan su tun yanzu. Bai yi sauri ku tsaya tsaye ba. Ga abubuwan da zamu iya yi.
Ku tambaye tambayoyi
Tunda babban yaya ta dan girme mu, zai yi sauki muyi mata magana. Idan tana aiki da kyau, mu walwala mu tambaye ta tambayoyi. Ya ta kai wannan matsayin? Ta koya wani takamammen kwarewa ne?. Menene tafi so akan sa? Idan muka shaku da babban yaya, zamu iya tambaya akan albashin ta.
Mu kala Mu koya
Idan muka samu kudi, yakamata muyi aiki sosai domin mu adana shi. Mu saka wa babban yaya ido. Tana aiki a babban ofishi, mai yiwuwa tana tashiwa da asuba domin ta kai aiki da wuri. Idan tana da karamar sana’a, maiywuwa tana karban aiki da safe kuma tana tabbata cewa ta ajiye alkawarin ta wa abokan cinikin ta. Idan muna da horaswa kamar ita, muma zamu ci nasara.
Yar uwa tafi sanin komai
Kafan mu samu kudi, zai yi taimako mu san aikin daya fi dacewa damu. Wanda ya dace da muradin mu da kuma yanayin mu. Ata nan, zamu iya samun riba daga yin abun da muke so. Kuma idan bamu san ko menene ba, babban yaya zata iya taimakon mu. Ta san mu fiye da kowane mutum. Zata iya taimakon mu gano muradin mu da kuma shafgar mu. Zata bamu shawara akan aikin yi da zai tsirata mu. Kada ku damu idan kuka kasa gano muradin ku yanzu, ku cigaba da gwada abubuwa daban-daban, zai zo muku.
Kuyi ajiya da hikima
Hankalin kowane mutum zai iya daukewa dan kudi. Shiyasa muke bukatan maida hankali da kuma yin ajiya da kyau. Mu tamabaye babban yaya akan asusun ajiya na kan waya. Ko kuwa dabaru akan ajiyen kudin mu. Ta taba masaniyar wannan. Saboda haka zata iya bamu shawara. Za mu kula da abubuwan da take fadi. Sai mu karanta su a kai a kai. Me zamu yi da bamu da babban yaya?
Ku tuna, tsiratar ku yazo farko koda menene. Idan wani ya baku shawarar yin wani aiki da baku yarda da ba, ku kai rahoto a wajan wani amintaccen babban mutum nan take. Kuma idan baku shirya samun kudi ba yanzu, ku dauka lokacin ku. Zaku iya farawa a lokacin da kuke so.
Menene kuma kuka koya daga yayin ku a gida? Gaya mana a wajan sharhi.
Share your feedback