Yadda Demi Akin take rayuwar da take so a shafin yanar gizo gizo

Da kuma abubuwa da zamu iya koya daga wajan ta

Kuna son hoton nan na kasa? Waya ne akan marikin waya da aka yi daga takarda!

demi_2.jpg

Muna tunanin wannan ya hadu kuma, yarinyar data yi wannan ta hadu sosai. Shiyasa muka yanke shawara muyi mata magana!

Sunnan ta Demi Akin kuma tana sanya nata rubutun a yanar gizo gizo Inda zamu iya koyan kwarewa da dabaru masu muhimmanci harda yadda zamu yi sana’ar hannu dabam-dabam wa kanmu, da wadanda muke kauna, har da wanda zamu iya saidawa.

Mu karanta mu kara koya akan ta.

Dan Allah ki kara bamu bayanin ki
Suna na Demi Akin kuma ina yin kayan yayi da kuma sanya rubutun abubuwan da zan iya yi da kai na. Ina da digiri na injiniya. Ina zama a Abuja da iyali na. Ni kadai ce mace kuma ni ce na farko a cikin yara uku. Abu daya dake saka ni farin cikin shine kayan yayi da kuma sana’ar hannu. Ina son yin amfani da hannu na na kirkira abubuwa. Shiyasa na siyo wa kaina keken dinki ko da lokacin da bani da masaniyar yin dinki.

demi_3.jpg

Kara bamu bayanin rubutun shafin yanar gizo gizon ki
Na fara rubutu a shafin yanar gizo gizo na a shekaru uku da suka wuce da wani buri dabam. Da fari, na so ya zama akan kayan yayi ne kawai. Amma da shekaru suka wuce na lura cewa duk da cewa ina son kayan yayi, nafi son sana’ar hannu da kuma kayan yayi da zan iya yi da hannu na. Shiyasa na fara rubutun yin abubuwa da kai na a shafin yanar gizo gizo na cikakken lokaci a tsakiyar shekarar 2016, kuma tun lokacin, na kara kaunar yin rubutu a yanar gizo gizo na.

Yanzu, a jimla daya zan iya fadi cewa rubutun da nake sanyawa a shafin yanar gizo gizo na akan nawa tsarin kaya ne da kuma aikin abubuwan da nake yi da kai na.

Kina bukatan kudi sosai domin ki fara sanya naki rubutu a shafin yanar gizo gizo?
Baku bukatan kudi kafan ku fara ( saidai na samun yin amfani da yanar gizo gizo). Zaku iya fara naku rubutun a shafin wordpress.com ta yin rijista kamar yadda kuka yi a facebook ko kuwa Instagram. Haka na fara nawa rubutun shafin yanar gizo gizon.

Yaushe kika fahimta cewa kina son ki kasance mai kirkira abubuwa da kuma gwada sabobin abubuwa?
Na fahimta tun da nake karamar yarinya. A gaskiya, iyaye na kawai zasu iya gaya muku lokacin dana fara nuna halayye na na kirkira abubuwa. Ni ce wannan yar yarinyar da almakashi a hannu koda yaushe, ina yanke kaya na kuma na kammala su. Da nake shekaru goma sha daya na fara nawa sana’a wanda nake amfani da takarda nayi kati. Duk inda na samu kai na, ni ce wannan yarinyar da ake samu ta kirkira wani abu. Ina ganin kasancewa kwararriya abu ne da aka haife ni da.*

DEMI4.jpg DEMI_5.jpg

Ya kike samun ra’ayi wa sabobin aiki?
Ina bin wasu masu sanya rubutun abun da suke yi da kan su a shafin yaran gizo gizo. Ina samu wahayi daga wajan su wasu lokuta. Mai yiwuwa na ga wani abu ko kuwa wani kyale sai hikimar ya zo mun kai. Misali daya shine aikin fifitar atamfa dana sanya shafin yanar gizo na a shekarar daya wuce. Na ga wata mai sanya rubutu a shafin yanar gizo da irin sa a taron kayan yayi da zane na jihar Lagos, amma tace ta siyo nata a kasar Ghana. Sai na zauna na minti kadan na karanta zanen fifitar, bayan makonni kadan nayi wa kaina irin sa. Ra’ayi na wahayi da zuwa a hanyoyi da yawa.

demi_6.jpg

Zaki iya tunanin mutanen da suka goyo bayan kwarewar ki?
Musamman iyali na. Da nake karama mahaifina na yawan bani kudin yin yawancin aiki na. Zai siyo mun takardu na yin sana’ar hannu na takarda kuma ya siyo sauran abubuwa da nake bukata. Mahaifiyata zata tuka ni zuwa wani shagon sarrafa abubuwa duk sanda nake son siyan wani abu. Koda yaushe zasu bani shawarar aikin da zan iya yi. Abokai na na shafin yanar gizo na bani goyon baya. Wasun su na tura mun abubuwa da sauran masu zane ke yi a Instagram, zasu ce “Demi, ina ganin zaki iya yin wannan” ko kuwa su ce “ wannan aikin zai yi kyau ki yi”.

Ina ganin goyon bayan nan na nan amma da fari, ban gaya wa mutane aniya na ba. Ni ba mai yawan gaya wa mutane abun da nake son nayi bane har sai na tabbata. wannan saboda bana son a sanyaya gwiwa na ne. Duk da haka, na san cewa goyon baya nada muhimmanci a duk abun da kuke son kuyi. Shiyasa nake koya wa kaina gaya wa mutane koda ina ganin kamar ra’ayi na bai da kyua, dan ban san inda zan iya samun taimako ba.

demi7.jpg

Akwai wanda ya taba gaya miki wani abu daya sanyaya gwiwar ki?
Akwai wata abokiyata data taba sanyaya gwiwa na dana fara sanya rubutun shafin yanar gizo gizo a shekarar 2014. Na dan yi bakin ciki saboda naji kamar bani da abun da zan iya badawa saboda akwai sauran masu sanya rubutu a shafin yanar gizo gizo. Muka daina abokantaka a cikin shekarar 2015 kuma a karshen shekara na fara nawa rubutun shafin yanar gizo.

Wanne shawara zaki iya bawa Springters dake da babban buri da kuma rayuwar su a gaban su?
Kada ku bari wani ya sanyaya gwiwar muradin ku amma kuma ku saurarre shawara idan kuna hanyar cimma burin ku. Ba dukka shawara zaku bi ba amma duk kalmar da aka fadi nada muhimmanci. Wasu lokuta shawara mara kyau na iya zama kwarin gwiwa mafi inganci da zai nuna wa mutumin cewa sunyi kuskure. ,br>
Kuma kada ku gaya wa kanku cewa kun kankanta ku fara. Na tuna sanda nake shekaru goma sha shida ina tunanin cewa ina da sauran lokaci kafan nayi girma – Nayi kuskure kuma ina ji dama na fara abubuwa da yawa da nake yin yanzu da sauri kuma shekaru na ishirin da uku ne yanzu.

demi8.jpg

Toh, yanzu mun samu wahayin bin burin mu da kwarewar mu bayan karanta wannan. Kuma muna fatan cewa kuma kun samu wahayi. Ku gaya mana yadda kuka samu wahayi a sashin sharhi.

Share your feedback